logo

HAUSA

Faraministan Isra’ila: Rundunar sojan kasar za ta fitar da dukkanin karfin soja domin daidaita kungiyar Hamas

2023-10-08 09:26:39 CMG Hausa

Da safiyar ranar 8 ga wata, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa, rundunar sojan Isra’ila za ta fitar da dukkanin karfin soja domin daidaita kungiyar Hamas.

A daren ranar 7 ga wata, ma’aikatar harkokin kare kasa ta Isra’ila ta fidda sanarwa cewa, sojojin Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare ta sama ga dakarun kungiyar Hamas dake yankin Gaza. Ta kuma kara da cewa, tun safiyar ranar 7 ga wata, gaba daya, kungiyar Hamas ta harba boma-bomai sama da 3000 ga yankunan dake cikin Isra’ila, kana, wasu dakarun kungiyar Hamas sun shiga unguwannin Isra’ila sama da guda 20 dake kusa da kan iyakar yankin Gaza, inda suka bude bindigogi ga jama’ar Isra’ila. Kawo yanzu, dakarun kungiyar Hamas sun yi garkuwa da sojoji da fararen hular Isra’ila da dama, sun kuma shigar da su cikin yankin Gaza. Sanawar ta kuma bayyana cewa, hare-hare na wannan rana sun riga sun haddasa rasuwar mutane sama da 200, yayin da mutane sama da 1000 suka jikkata cikin Isra’ila.

Bugu da kari, bisa labarin da aka samu daga bangaren Falasdinu, hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai ga yankin Gaza sun haddasa rasuwar mutane 232, yayin da mutane kimanin 1700 suka jikkata cikin yankin. Ban da haka kuma, ’yan Falesdinu guda 6 sun rasu sakamakon musayar wuta dake tsakaninsu da sojojin Isra’ila a garin Ramallah da dai sauran wuraren dake yammacin kogin Jordan. (Maryam)