logo

HAUSA

Najeriya za ta noma hekta dubu 70 na gonar alkama yayin noma rani a bana

2023-10-08 15:23:50 CMG Hausa

Ma’aikatar gona da albarkar kasa ta tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, karkashin shirin wadata kasa da abinci, an tanadi fili mai fadin hekta dubu 70 domin gudanar da noman alkama yayin noman rani na bana da za a fara daga watan gobe na Nuwamba.

Ministar ma’aikatar, Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Abuja da yammacin Juma’a 6 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ministan gonar na tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya ce, za a samar da filayen noma ne a shiyoyin kasar da suka yi fice wajen noman alkama, kuma ana sa ran samun tan dubu 875 na alkama, inda za a adana ta a ma’ajiyar abinci ta gwamnati.

Haka kuma ministan ya ce, an samar da wadataccen takin da zai tallafawa nasarar noman rani na bana, yayin da kuma tuni aka fara tanadin noman damunar badi.

Ministan gonar na tarayyar Najeriya ya kara da cewa, noman alkama na shekarar 2023 wani bangare ne na shirin bunkasa noma na kasa dake samun tallafin bankin raya kasashen Afrika.

Karkashin wannan shiri dai, akwai bayar da horo ga malaman gona wadanda su kuma za su koma domin horas da manoman rani bisa hadin gwiwa da gwamnatocin jihohin da suke noman alkama da kuma sauran abokan hulda kamar kamfanonin sarrafa fulawa.

Ya ce, ma’aikatar gonar za ta shigo da masu ruwa da tsaki cikin harkokinta domin ta haka ne kawai za a iya cimma burin shugaban kasa ta fuskar ci gaban ayyukan gona.

“A sakamakon haka yanzu ma’aikatar tana gudanar da wani nazarin bincike kan masu ruwa da tsaki da za su samar da wata taswira wadda za ta zayyano adadin wadanda suke taka rawa kan sha’anin noma ta hanyar tantance abun da suke nomawa, wuraren da suke yin noman da kuma yadda suke gudanar da noman, sannan kuma wane irin fa’idoji manoman suke samu, kama daga kananan, da manyan da masu sarrafa kayan amfanin gona da ’yan kasuwa da kuma kamfanoni masu zaman kansu.” (Garba Abdullahi Bagwai)