logo

HAUSA

Adadin Wadanda Suka Mutu Sanadiyar Girgizar kasar Afghanistan Ya Zarce Dubu Biyu

2023-10-08 16:06:15 CGTN Hausa

Majiyoyin gwamnati sun bayyana cewa, mutane 2053 ne suka mutu, yayin da fiye da 9200 kuma suka jikkata, sakamakon wata girgizar kasa mai karfin gaske da ta afku a lardin Herat da ke yammacin kasar Afghanistan jiya Asabar.

A cewar cibiyar bayar da bayanai kan girgizar kasa ta kasar Sin, girgizar kasa guda biyu masu karfin maki 6.2 ne suka afkawa kasar Afghanistan a jiya.

Da farko dai, wata sanarwar da hukumar kula da bala'o'i ta kasar Afghanistan ta fitar na cewa, gidaje da dama sun lalace ko kuma sun ruguje gaba daya sanadiyar girgizar kasar.

Bayanai na cewa, an aika da tawagogin aikin ceto zuwa yankunan da lamarin ya shafa, kana an umurci jami’an gwamnatin lardin, da su hada kai da kungiyoyin agaji domin kai agajin jin kai ga iyalan da girgizar kasar ta shafa.(Ibrahim)