logo

HAUSA

Aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” ya samar da sabbin damammaki ga duniya a cewar kusoshin siyasa na kasashe da dama

2023-10-07 16:04:32 CMG Hausa

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru goma, da kasar Sin ta gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”. Kuma ya zuwa yanzu, shawarar ta zama sanannen abu da jama'a ke amfani da shi a duniya, tun daga karfafa tushenta har zuwa tabbatar da ita, wadda ta haifar da karfin ingiza ci gaba mai dorewa ga kasashe da dama.

A yayin da suke zantawa da manema labaru na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin a kwanan baya, a birnin New York na kasar Amurka, kusoshin siyasa na kasashe masu yawa sun bayyana cewa, aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", ya kawo sabbin damammakin samun ci gaba ga duniya, kuma kasashensu na son kara yin la'akari da damar kasuwanci irin ta samun moriyar juna tare da kasar Sin, don inganta matsayin hadin gwiwa.

Game da hakan, shugaba Julius Maada Bio na kasar Saliyo ya ce, duk wani alkawari da kasar Sin ta yi, ba ta taba gindaya wani sharadi na cika shi ba, kuma shawarar “ziri daya da hanya daya” na da matukar muhimmanci, musamman ta fuskar gina ababen more rayuwa.

Wadannan gine-gine ba wai kawai sun samarwa mutane damar samun hidima daga gwamnati cikin sauki ba ne, har ma sun taimakawa kasarsu wajen samun ci gaban aikin gona ta hanyar kiyaye muhalli, da kuma baiwa kasarsu, da al'ummarsu damar shiga kasuwa yadda ya kamata.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Hassan Shoukry, cewa ya yi sun yi imani manufar dunkulewa da juna ta shawarar "ziri daya da hanya daya", za ta yi tasiri mai kyau, ciki har da bunkasa cinikayya, da hadin gwiwar kasuwanci, da damar zuba jari da dai sauransu, kuma ci gaba da raya shawarar zai ba da kwarin gwiwa ga Masar, wajen cimma burinta na samun bunkasuwa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)