logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da gidaje guda 40 ga ’yan gudun hijarar dake jihar Zamfara

2023-10-07 15:11:31 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta samar da gidaje guda 40 a jihar Zamfara domin amfanin ’yan hijirar dake zaune a sansanoni daban daban.

A lokacin da take mika rukunin gidajen ga gwamnatin jihar Zamfara a garin Gusau yayin wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar, ministar harkokin jin kai da yaki da talauci ta Najeriya Dr Betta Edu ta ce, kowane gida zai wadaci mutum mai iyalai 9 kuma nan gaba kadan za a kawo musu tallafin kayan abinci da tallafin koyon sana’o’i.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Dr Betta ta yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya za ta gina karin wasu gidaje a shiyoyi uku na jihar ta Zamfara domin dai ’yan gudun hijira kasancewar jihar ta Zamfara tana daya daga cikin jihohi dake da mafi yawan ’yan gudun hijira a Najeriya.

“Muna son mu tabbatarwa al’ummar jihar Zamfara, sannan kuma zan yi amfani da wannan dama wajen kira ga kasashen duniya, kamar yadda nake fada a kowane lokaci tashe-tashen hankula bai tsaya kawai ga jihohin dake arewa maso gabas ba, muna da wurare a arewa maso yamma kamar jihar Zamfara, muna da su a arewa ta tsakiya kamar jihar Benue da sauran sassa na Najeriya, a sabo da haka muke kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su hada kai da gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatocin jihohi domin dai tabbatar da ganin an yi kokarin kai dauki ga ’yan gudun hijira musamamn ta fuskar samar da muhalli, kiwon lafiya, ilimi, kyautata rayuwa da kuma samar da horon koyon sana’o’in dogaro da kai da sauransu.”

A jawabinsa, gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan ya yabawa ministar yayin bisa ziyartar jihar da ta yi tare kuma da mika makullan gidajen ga gwamnati, inda ya ce babu shakka samar da gidajen zai rage wahalhalun da ’yan gudun hijirar ke fuskanta a akasarin sansanonin da aka tsugunar da su.

Ya kuma yi fatan cewar za a samar da karin wasu gidajen domin biyan bukatun dubban ’yan gudun hajirar dake zaune a jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)