logo

HAUSA

Tashar Lekki na sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin yammacin Afirka

2023-10-07 21:05:44 CMG

Daga Lubabatu Lei

Yau ina tare da wani albishirin da zan so in gutsura muku. Tashar jiragen ruwa ta Lekki da ke birnin Lagos, ta riga ta samar da guraben aiki sama da 3,000 ga al’ummar wurin tun bayan da ta fara aiki a hukunce a watan Afrilun wannan shekara.

An ce, tashar Lekki na iya samar da guraben aiki kimanin dubu 170, kuma sama da kaso 90% daga cikinsu an samar da su ne ga mazauna wurin.

Har wa yau, kasancewarta tasha mai zurfin ruwa ta zamani irinta ta farko a Nijeriya, wadda kuma ke daya daga cikin tashoshi masu zurfin ruwa mafiya girma a yammacin Afirka, yadda aka fara aiki da tashar Lekki, ya daidaita matsalolin koma bayan ababen tashar Lagos da ke yi wa ci gaban cinikin da Nijeriya ke yi da kasa da kasa tarnaki, wadda ta yi matukar kyautata kwarewar birnin Lagos ta fannin shige da ficen hajjoji.

Ban da haka kuma, sakamakon yadda Nijeriya ta kasance kofar wasu kasashen da ke cikin Afirka, irinsu Chadi, da Nijer ta hadewa da teku, tashar ta Lekki, za ta kuma kara samar da karfin bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar.

Hadewa da juna ta bangaren manyan ababen more rayuwa, na daya daga cikin manyan burikan da ake neman cimmawa wajen aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, a wani kokari na sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin shiyya, da ma na duniya baki daya. Kasancewarsa daya daga cikin nasarorin da aka cimma, a gun taron kolin kasa da kasa karo na biyu kan shawarar ziri daya da hanya daya, tashar Lekki ba kawai ta taimaka ga ci gaban tattalin arzikin cikin gidan Nijeriya ba ne, har ma za ta zama muhimmiyar mahada ta teku, wanda hakan ya aza ingantaccen harsashi ga bunkasuwar tattalin arzikin Afirka baki daya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)