logo

HAUSA

Pushpa Kamal Dahal: Gasar wasannin Asiya na da muhimmiyar ma’ana ga al’ummomin kasar Nepal

2023-10-07 15:32:00 CMG Hausa

A yayin zantawarsa da ’yar jaridar Babban Gidan Rediyo da Talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Nepal Pushpa Kamal Dahal, ya bayyana cewa, ya yi farin ciki sosai da halartarsa bikin bude gasar wasannin Asiya, kasancewar a yayin bikin, ya zanta da shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, ’yan wasannin motsa jiki na kasar Nepal sun halarci gasar wasannin Asiya cikin himma da kwazo, tun daga gasar ta karon farko. Kuma a wannan karo ma kasar Nepal ta tura ’yan wasannin motsa jiki sama da dari 2 zuwa kasar Sin domin halartar gasar. Kasancewar gasar na da muhimmanci sosai ga ’yan wasanni, da al’ummomin kasar Nepal, har ma da shi kansa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)