logo

HAUSA

Yadda aka farfado da tsohon birnin Khiva

2023-10-06 20:35:24 CMG Hausa

“Ina so in ba da jakar zinare, don kawai in kalli Khiva.” Wani tsohon karin magana na Tsakiyar Asiya ya bayyana daukakar wannan tsohon birnin mai tsawon tarihin shekaru dubu a baya. Wannan muhimmiyar tashar da ke tsohuwar hanyar siliki ta kasance wurin da 'yan kasuwa ke taruwa, lamarin dake kiyaye wadatar wannan hanyar kasuwanci mai tsayi.

A shekarar 2022, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasar Uzbekistan karo na uku, ya mika wa shugaban kasar Shavkat Mirziyoyev wata kyauta ta musamman ta kasa, wato karamin samfurin tsohon birnin Khiva da kasashen Sin da Uzbekistan suka yi wa kwaskwarima tare. Bayan wannan kyautar kasa akwai wani kyakkyawan labari game da yadda ake sa kaimi ga mu'amalar wayewar kai tsakanin Sin da Uzbekistan ta hanyar gudanar da diflomasiyya da shugabannin kasashen biyu ke yi.

Tsohon birnin Khiva shi ne aikin kiyaye al'adun gargajiya na farko da kasar Sin ta aikata a tsakiyar Asiya. To sai dai kuma saboda rashin gyare-gyare, wasu tsoffin gine-gine a tsohon birnin na ci gaba da tabarbarewa har ma suna gab da rugujewa.

A cikin shekaru shida da aka yi hadin gwiwa tsakanin Sin da Uzbekistan wajen gudanar da aikin gyare-gyaren, "likitocin kayayyakin al'adu" na kasar Sin sun yi aiki kafada da kafada da jama'ar kasar don maido da tsoffin gine-gine ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tare da yin iyakacin kokari wajen kiyaye gaskiya, da kuma cikakkun bayanan tarihi masu daraja na tsohon birnin Khiva.

"Ana yin mu’amalar wayewar kai ne saboda kasancewar bambance- bambance, ana koyi da juna ne saboda yin mu’amala, ana kuma samun ci gaba ne saboda a koyi da juna." "Ba wai kawai mun sanya wayewar kanmu mai cike da kuzari ba, har ma mun samar da yanayi mai kyau don ci gaban wayewar kan sauran kasashe, ta yadda lambunan wayewar kan duniya za su kasance cike da furanni." A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi hadin gwiwa tare da kasashe 17 bisa raya shawarar "ziri daya da hanya daya" don gudanar da ayyukan binciken kayayyakin tarihi guda 33 na hadin gwiwa, tare da sa kaimi ga hadin gwiwa a fannin kiyayewa da gyare-gyaren kayayyakin tarihi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)