logo

HAUSA

MDD ta bayyana damuwa game da hare-hare a Syria

2023-10-06 17:07:59 CMG

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar damuwa dangane da harin jirgi mara matuki da aka kai kwalejin horar da sojoji a Syria da kuma na ramuwa da dakarun gwamnati ke kai wa.

Da yake ganawa da manema labarai a jiya Alhamis, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ruwaito Antonio Guterres na yin Allah wadai da kakkausar murya game da rikice-rikice a Syria, yana mai kira ga dukkan bangarori su martaba hakkokin dake wuyansu bisa dokokin kasa da kasa.

Rahotanni sun ce mutane akalla 100 ne suka mutu a ranar Alhamis yayin wani hari da aka kai kwalejin horar da sojoji dake Syria. Wasu jirage mara matuka ne suka tada bam din, mintoci kalilan bayan ministan tsaron kasar ya bar wajen bikin yaye sojoji da aka yi a kwalejin.

Wannan daya ne daga cikin munanan hare-hare da aka kai wa sansanin sojan Syria, kuma karo na farko da aka yi amfani da jirage marasa matuka dauke da makamai wajen kai hari a kasar, tun bayan fara yakin basasan da ya shafe shekaru 12.

Ma’aikatar tsaro da ta harkokin waje na Syria, sun lashi takobin mayar da martani mai karfi. Kuma tuni dakarun gwamnatin Syria suka shafe tsawon wannan rana suna kai hare-haren bam a yankin Idlib dake karkashin bangaren adawa. (Fa’iza Mustapha)