logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi karin haske kan ra'ayi da matsayin kasarsa game da yanayin tsaro na kasa da kasa da kwance damarar makaman nukiliya

2023-10-06 17:34:59 CMG Hausa

Sun Xiaobo, shugaban tawagar kasar Sin dake halartar kwamitin kwance damara da tsaro na kasa da kasa (kwamitin farko) na babban taron MDD karo na 78, kana daraktan sashen kula da harkokin takaita yaduwar makamai na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi jawabi a yayin babban taron muhawara na MDD da aka yi a jiya Alhamis, inda ya yi cikakken bayani kan ra’ayin kasarsa a fannin yanayin tsaron kasa da kasa, da manufofin da kasar ke dauka kan wasu batutuwan da suka shafi zaman lafiya a duniya bisa manyan tsare-tsare, da kawar da makaman nukiliya, da hana yaduwarsu da sauransu.

Jami’in ya ce, a bana ake cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil'adama. Kuma tarihi da ayyuka sun tabbatar da cewa, duniyar yau al’umma ce mai makoma guda da ta samu wadata da asara. Ya ce shawarar samar da tsaro a duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, wata al’ada ce ta fahimtar al’umma mai makoma daya ga bil’adama a fannin tsaro, kuma ya samar da mafita irin ta kasar Sin wajen samun dauwamammen zaman lafiya a duniya.

Baya ga haka, jami’in ya jaddada cewa, a yayin da ake fuskantar sabbin kalubale a sabon yanayin da ake ciki, kamata ya yi sassa daban daban su kokarta su kiyaye zaman lafiyar duniya bisa manyan tsare-tsare da rage hadari a fannin. Kuma ya kamata a aiwatar da manufar rashin kasancewa na farko wajen amfani da makaman nukiliya a duk duniya. Bugu da kari, a dage wajen kare tsarin kawar da makaman nukiliya na kasa da kasa da hana yaduwar makaman bisa yarjejeniyar hana yaduwarsu, da inganta manyan manufofin yarjejeniyar cikin daidaito. (Mai fassara: Bilkisu Xin)