logo

HAUSA

An samar da cibiyar nazari akan cusa akidar karatun litattafai da harkokin bincike ta kasa a jami’ar Bayero

2023-10-05 16:11:36 CMG Hausa

Jami`ar Bayero dake Kano a arewacin Najeriya ta samar da cibiya ta kasa kan bukasa sha’anin bincike da cusa akidar karatun littattafai a tsakanin dalibai da malamai.

Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ne ya jagoranci kaddamar da cibiyar a harabar sabuwar jami`ar, ya ce wannan yunkuri zai taimake su kan su malamai a dukkan matakai wajen kara fadada sha`anin bincike da zumma inganta kwarewar su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ita dai wannan cibiya ita ce irinta ta farko a Najeriya wadda zata rinka fito da tsare tsare da dabarun sauya tunanin dalibai tun daga makarantun firamare wajen rungumar halayyar karance karancen littattafai.

Yayin bikin an gayyato masana a fannonin ilimi daga cibiyoyin ilimi daban daban dake kasashen duniya inda suka gabatar da mukaloli.

A lokacin da yake jawabi shugaban jami’ar Bayero yace wannan cibiya za ta yi kokarin bullo da saukakan hanyoyi da kananan yara za su rinka nuna sha`awar karatun littattafai.

“An kafa wannan cibiya ce saboda ayi kokari a samu yara tun suna kanana su tashi da al`ada ta yin karatu, idan muka yi sa a aka yi wannan to zamu ga yaran mu a gaba nan da shekara 20 ko 15 zasu girma tare da tashi da al`adar yin karatu”

Yace haka kuma cibiyar zata rinka bayar da horo ga malamai tare da ba su kayan aiki ta yadda za su ilimantar da daliban su dabarun gudanar da bincike-bincike.

A nata jawabin, daraktar cibiyar Farfesa Talatu Musa Garba tace sakamakon yawaitar fasahohin zamani wajen karatu a makarantu, cibiyar ta yanke shawarar jagorantar taron karawa juna sani inda aka gayyato masana domin fito da mahajojin da zasu yiwa dalibai jagoranci wajen yin karatu ta amfani da kafofin zamani kari akan karfafa masu gwiwar daukar littattafai suna karantawa kai tsaye.

“Duk in aka yi maganar karatu ana maganar ka dauki littattafi ka karanta ne, amma yaran mu yanzu sun fi son su yi karatu ta wayoyin hannu ko a kwamfuta ba su cika son litttafi ba, hatta a jami’o’in mu yanzu dalibai maimakon su karanta littattafan da suka dauki darasi, idan ka basu aikin gida sai kawai su tafi kafofin internet su kwafo su kawo maka.”(Garba Abdullahi Bagwai)