logo

HAUSA

Tsige McCarthy daga mukaminsa ya nuna me ake nufi da "Dimokradiyyar Amurka"

2023-10-05 17:01:38 CMG Hausa

A ranar 3 ga watan Oktoba, ‘yan majalisar wakilai da ke karkashin jagorancin jam’iyyar Republican, suka kada kuri'u 216 na amincewa da 210 na kin amincewa don tsige kakakin majalisar Kevin McCarthy daga mukaminsa.

A ranar 1 ga watan Oktoban kowace shekara ne a kan fara gudanar da kasafin kudin gwamnatin tarayyar Amurka.

Tun daga watan Satumbar bana, takaddamar da ke tsakanin jam'iyyun siyasa biyu a Amurka game da kasafin kudin sabuwar shekara ke kara kamari. A ranar 30 ga wata, a matsayinsa na kakakin majalisar wakilai, McCarthy ya yanke shawarar hada kai da 'yan jam'iyyar Democrat, don zartar da kudurin bayar da kudi na wucin gadi. Bugu da kari, kudurin bai hada da shawarwarin masu ra'ayin rikau na jam’iyyar Republican ba, na rage yawan kudin da gwamnatin tarayya ke kashewa da kuma tsaurara matakan kula da iyakokin kasa. Hakan ya kara rura wutar rikicin da ke tsakaninsa da masu ra’ayin rikau a jam’iyyar Republican.

A daren ranar 2 ga watan Oktoban, dan Republican mai ra’ayin rikau wato Matt Gaetz, ya gabatar da kudurin tsige Kevin McCarthy, bisa dalilin dake cewa “Yana hidimtawa jam’iyyar Democrat.”

Jam'iyyar Republican tana da kujeru 221 a majalisar wakilai, wanda ya zarce kujeru 212 na jam'iyyar Democrat. Duk da haka, saboda "tawayen" wasu 'yan majalisar Republican takwas masu ra'ayin rikau, daga karshe majalisar ta tsige McCarthy.

Kamar yadda manazarta da dama suka yi nuni, adawar da ake yi tsakanin jam'iyyun siyasa a Amurka da kuma yadda ake gwabza fada tsakanin jam'iyyun na daga cikin muhimman dalilan da suka saukar da McCarthy daga mukaminsa. Saboda rikicin jam’iyyun, wasu mambobi masu ra'ayin rikau kadan na iya yin tasiri a kan zaben shugaban majalisar wakilai, wannan alama ce da ke nuna yanayin siyasar Amurka a halin yanzu.

Wannan lokacin ne da siyasar Amurka ta yi amfani da muradun son kai na wasu tsirarun mutane, kuma lokaci ne da aka mayar da dimokuradiyyar Amurka matsayin "wasan mulki," to ta yaya za a iya amincewa da "labarin dimokuradiyya" da 'yan siyasar Amurka suka rubuta? (Mai fassara: Bilkisu Xin)