logo

HAUSA

Sin da wasu kasashe 80 sun yi kira da a kyautata tsare-tsaren tallafawa tsoffi

2023-10-05 16:54:04 CMG

Kasar Sin ta gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin wasu kasashe 80, yayin zama na 54 na majalisar kula da hakkokin bil adama ta MDD, wadda ta yi kira da a kyautata tsare-tsaren tallafawa tsoffi.

Da yake gabatar da sanarwar a jiya Laraba, Chen Xu, shugaban tawagar kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ya ce adadin tsoffi na karuwa a fadin duniya, haka kuma ana kara samun rashin isassun tsare-tsaren tallafa musu, ciki har da rashin tsari mai dorewa da rashin daidaito a fannin kula da su a tsakanin yankuna da kuma wariyar shekaru da ake nuna musu.

Sanarwar ta jaddada cewa, kowa da kowa ciki har da wadanda suka manyanta, su na da hakkin samun tallafi, ta yadda za su yi rayuwa cikin mutunci da shiga ana damawa da su cikin harkokin al’umma.

Har ila yau, ta yi kira ga kasashe su dauki kwararan matakai na magance tsaikon da tsoffi ke fuskanta ta fuskar matakan samun tallafi, ta yadda ba za a bar kowa ba. (Fa’iza Mustapha)