Kazakhstan, kasa marar ruwa mafi girma a duniya, tana da nata hanyar shiga teku
2023-10-05 17:45:30 CMG Hausa
A ranar 7 ga watan Satumban shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a jami'ar Nazarbayev dake kasar Kazakhstan mai taken "Sada zumunci tsakanin jama'a da samar da makoma mai kyau tare", inda a karo na farko ya gabatar da raya shawarar "ziri daya da hanya daya" .
Kasar Kazakhstan ta zama wuri na farko da aka gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma inda aka fara hadin gwiwa bisa shawarar.
A sakamakon haka aka kafa wani sansanin jigilar kayayyaki na kasa da kasa a Lianyungang na kasar Sin mai nisan kilomita sama da 4000 daga Astana, babban birnin kasar Kazakhstan. Aikin "sansanin hadin gwiwa na jigilar kayayyaki na Lianyungang a tsakanin Sin da Kazakhstan" shi ne aikin zahiri na farko da aka fara aiwatarwa bayan gabatar da raya shawarar "ziri daya da hanya daya". Tun daga wannan lokacin, Kazakhstan, kasa marar ruwa mafi girma a duniya, take da tashar da za ta tashi daga Tekun Pasifik.
A cikin shekaru 10 da suka gabata, sansanin ya zama cibiyar jigilar kayayyaki ta kasa da teku a tsakanin Asiya da Turai. Kazakhstan kuma ta zama muhimmiyar tashar sufuri da ke hada Asiya da Turai, jiragen kasa na jigilar kayayyaki na Sin da Turai suna wucewa ta nan akai-akai.
Ana ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Kazakhstan wajen gina shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda ya zama misali na samun moriyar juna da samun nasara tare a tsakanin makwabta kuma abokai. (Mai fassara: Bilkisu Xin)