logo

HAUSA

An fara sakin zagaye na biyu na dagwalon nukiliya na Fukushima

2023-10-05 16:55:44 CMG

Japan ta fara zagaye na biyu na sakin gurbataccen ruwa dagwalo daga tashar nukiliya ta Fukushima Daiichi, a yau Alhamis.

Kamfanin samar da Lantarki na Tokyo ya shirya zuba kimanin ton 7,800 na dagwalon nukiliya cikin teku a tsawon kwanaki 17, adadin ya yi daidai da wanda ya saki daga ranar 24 ga watan Augusta, zuwa 11 ga watan Satumba. (Fa’iza Mustapha)