logo

HAUSA

Rundunar sojojin Nijar ta sanar da mutuwar sojoji 29 a cikin wani harin ta’addanci a Takanamat yankin Tahoua

2023-10-04 16:21:49 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, wani harin ta’addanci cikin daren ranar 2 zuwa 3 ga wata ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 29 da jikkata wasu, a yankin Tahoua mai iyaka da kasar Mali, a cewar wata sanarwa ta ma’aikatar tsaron kasar Nijar karkashin sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

Shi dai wannan kazamin harin ya faru ne a kauyen Takanamat cikin jahar Tillia da ke cikin yankin Tahoua a kusa da iyaka da kasar Mali.

Shi dai wannan hari shi ne mafi muni da aka samu a wannan yanki na Tahoua tun bayan da sojoji suka yi juyin mulkin a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, inda kuma matsalar tsaro na daya daga cikin manyan dalilan da suka sa sojoji karbe iko daga hannun gwamnatin fararen hula.

Daga karshe kwamitin ceton kasa na CNSP da gwamnatin rikon kwarya sun sake jaddada niyyarsu ta kawo karshen matsalar tsaro a cikin yankunan kasar Nijar da ke fama da matsalar tsaro da ta’addanci.

Mamane Ada, wakilin sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.