logo

HAUSA

Hatsarin kwale-kwale ya yi sanadin bacewar mutane 40 a arewacin Nijeriya

2023-10-04 16:53:11 CMG Hausa

Mutane akalla 40 ne aka bada rahoton sun bata, bayan wani kwale-kwale dauke da fasinjoji ya kife a kogin jihar Kebbi dake arewacin Nijeriya

Shugaban karamar hukumar Yauri ta jihar Kebbi Bala Mohammed, ya shaidawa manema labarai cewa, kwale-kwalen ya kife ne a ranar Litinin, yayin da yake dauke da fasinjojin 50 dake kan hanyarsu ta zuwa cikin kasuwa a yankin karamar hukumar Yauri.

Ya kara da cewa, kawo yanzu, fasinjoji 10 kadai aka ceto. Yana mai cewa kwale-kwale na ratsa yankin kogin da ya hada jihar Neja dake arewa maso tsakiyar kasar da jihar Kebbi, a lokacin da ya gamu da yanayin tafiyar ruwa mai karfi da ya yi sanadin hatsarin.

A nasa bangare, shugaban hukumar kula da agajin gaggawa ta jihar Neja, Salihu Garba, ya shaidawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar cewa, hukumomin yankin da na ayyukan agaji sun kaddamar da ayyukan ceto domin ganowa da ceto fasinjojin da suka bace. (Fa’iza Mustapha)