logo

HAUSA

Yadda yankunan cinikayya da masana’antu marasa shinge suke taka rawa wajen raya tattalin arziki

2023-10-04 08:00:04 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara zage damtse, wajen ganin an gina ingantattun yankunan cinikayya marasa shinge na gwaji (FTZs), inda ya bukaci wadannan yankunan da su kasance a sahun gaba wajen samar da sabbin damammaki, da tunkarar manyan kalubale. 

Xi, ya bayyana hakan ne a cikin wani umarni da ya bayar a baya-bayan game da inganta aikin gina yankunan cinikayya maras shinge na gwaji. Bayanai na nuna cewa, an gina irin wadannan yankuna cinikayya na gwaji a kasashen Afirka, kamar Lekki dake Najeriya, da Habasha, da Zambiya da sauransu.

Ya ce, wadannan yankunan cinikayya marasa shinge na gwaji, za su taka rawa dake zama abin misali, ta hanyar kara zurfafa bude kofa da mayar da hankali a fannin kirkire-kirkire da tsara matakan samun bunkasuwa da tsaro da tsara dokoki da suka shafi tattalin arziki da na cinikayya na kasa da kasa.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2013 ne, kasar Sin ta fara kaddamar da yankin cinikayya maras shinge na gwaji a Shanghai, kuma yanzu haka akwai irin wadannan yankuna a hukumance guda 21 da aka kafa a larduna da birane daban-daban na kasar. Aikin wadannan yankuna sun hada da kula da fitarwa da shigo da hajoji bisa manufofi na musamman, kamar tsarin cirewa da rangwamen haraji da dokokin kwastan da sauran dokoki masu nasaba da shigowa da fitar da kayayyaki tsakanin kasashen dake da hadin gwiwar cinikayya da kasar Sin.

Wadannan yankunan a cewar masana, sun taimaka wajen saukaka cinikayya da shiga wasu nau’o’in kayayyaki da samar da guraben ayyukan yi da sauransu, matakin da ya taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki. (Yahaya, Ibrahim/Sanusi Chen)