logo

HAUSA

McCarthy ya ce ba zai sake neman shugabancin majalisar wakilan Amurka ba

2023-10-04 16:03:57 CMG Hausa

Hambararren shugaban majalisar wakilan Amurka, Kevin McCarthy, ya shaidawa wani taron manema labarai da yammacin jiya Talata cewa, ba zai sake neman shugabancin majalisar ba, sa’o’i kadan bayan tsige shi daga mukamin saboda rikicin cikin gida na jam’iyyar Republican.

Kuri’a 216 na amincewa da 210 na kin amincewa da aka kada domin tsige shi, wadda ita ce irinta ta farko a majalisar, ta zo ne watanni kusan 9 bayan McCarthy ya lashe zaben shugabancin majalisar a wani yanayi mai ban mamaki bayan kada kuri’a har sau 15. Wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar da aka tsige shugaban majalisar wakilai yana tsaka da wa’adin mulki.

Wasu ‘yan Repulican 8 sun marawa ‘yan Democrat baya wajen kada kuri’ar tsige McCarthy daga matsayin, kasa da kwana guda bayan dan Republican mai ra’ayin rikau wato Matt Gaetz, ya gabatar da kudurin tsige shi.

Gaetz da wasu masu ra’ayin rikau na Republican, sun shafe makonni suna gargadin tsige McCarthy daga matsayinsa idan har ya dogara da ‘yan Democrats wajen amincewa da kudurin samar da kudaden harkokin gwamnati. (Fa’iza Mustapha)