logo

HAUSA

Me ya sa aka kasa shawo kan matsalar hare-haren bindiga a kasar Amurka?

2023-10-04 19:46:18 CMG

Daga Lubabatu Lei

    A jiya da dare,aka samu harin bindiga a jami’ar Morgan da ke jihar Maryland ta kasar Amurka, harin da ya jikkata wasu mutane biyar.

Hakika, hare-haren bindiga na kara addabar yara da matasa a kasar Amurka. Alkaluman da cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Amurka ta samar a kwanan baya sun yi nuni da cewa, hare-haren bindiga sun zarce hadurran mota har sun zo na farko a matsayin dalilin mutuwar yara da matasa a kasar.

Alkaluman sun shaida cewa, daga shekarar 2019 zuwa ta 2021, yara da matasan da suka halaka sakamakon hare-haren bindiga sun karu da kaso 50%, ko a shekarar 2021 kadai, kimanin kaso 19% na mutuwar yara da matasa na da alaka da hare-haren bindiga.

Lamarin da ya sa na tuna da wani hoton bidiyon da aka watsa ta yanar gizo a bara, wanda ya janyo cece-kuce daga masu kallonsa. Bidiyon ya nuna yadda wata ‘yar Amurka ta sayo wa danta mai shekaru 5 da haihuwa wata jakar karatu da za ta iya kare shi daga harbin bindiga, tare da horar da shi a gida kan yadda zai iya gudu daga hare-haren bindiga. Wadanda suka kalli bidiyon da dama sun ce, hakan abin bakin ciki ne. Babu shakka, sai dai gaskiyar lamarin da ya faru ya fi hakan bakanta wa mutane rai, alkaluman da cibiyar kididdigar harkokin ba da ilmi ta kasar Amurka(NCES) ta samar sun yi nuni da cewa, daga shekarar 2021 zuwa ta 2022, gaba daya an samu lamuran harbe-harben bindiga 327 a makarantun kasar, ciki har da na firamare da na sakandare, kuma 188 daga cikinsu sun haifar da mutuwar mutane ko jikkatarsu.

Hare-haren bindiga da ake ta samu a kasar ya sa al’ummar kasar ke ta kira ga gwamnati da ta dauki matakai na shawo kan matsalar, sai dai sakamakon yadda jam’iyyun siyasar kasar suke ta ja-in-ja da juna, da ma yadda masu kera bindigogi da ‘yan siyasa na kasar suke hada baki da juna, ya sa da wuya gwamnatin kasar ta fitar da ingantattun matakai da za su kai ga shawo kan matsalar.

Yara manyan gobe, abin kunya ne yadda kasar ta Amurka ta kasa kare yaranta daga hare-haren bindiga. Rayuka su ne tushen hakkin dan Adam, kuma abin takaici ne yadda hare-haren bindiga suke ta halaka ’yan kasar. (Mai Zane: Mustapha Bulama)