logo

HAUSA

Hutun cikar Sin shekaru 74 ya nuna ci gaban da kasar ta samu da wadatar al’ummarta

2023-10-03 19:23:34 CMG Hausa

Yanzu haka al’ummar kasar Sin suna hutu mai tsawo na kwanaki 8 da ya hada da hutun bikin tsakiyar kaka da kuma na zagayowar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, wadda a bana ake cika shekaru 74.

Wani abu da kan burge ni da al’ummar Sinawa shi ne, kishin kasa. Yadda a birnin Beijing kadai mutane kusan 300,000 suka yi tattaki zuwa dandalin Tiananmen a ranar Lahadi da safe domin murnar ranar kafuwar kasar, ya burge ni ainun. Kuma ba birnin Beijing kadai ba, har ma dukkan sassan kasar da ma al’ummomin Sinawa dake ketare, su kan gudanar da bukukuwa domin zuwan wannan rana, lamarin dake nuna matukar kaunarsu da kishinsu ga kasar, har ma da ci gaban da ta samu.

Haka kuma, wannan lokacin hutu ya kara tabbatar da ci gaban da kasar Sin ta samu tare da farfadowar harkokin yau da kullum bayan mummunar annobar da ta tsayar da kusan komai a duniya. Zan iya cewa, farfadowar harkokin ya samo asali ne daga jajircewar hukumomin kasar da shugabanci na gari da kuma kaifin basirar raya ta. Idan muka dauki lardin Hunan dake kudancin kasar Sin a matsayin misali, tafiye-tafiyen da aka yi da suka zarce miliyan 2.7 zuwa wuraren bude ido sama da 950 a ranar Asabar kadai, ya samar da kudin shigar da ya kai yuan miliyan 370, kwatankwacin dala milyan 50.7, wanda ya nuna karuwar kaso 49.1 akan na bara. Wannan ya kara tabbatar min da matakin kasar Sin na kokarin bunkasa tattalin arzikinta a cikin gida. Kasar Sin ta zabarwa kanta wata kyakkawar hanyar raya kanta cikin aminci da lumana.

Bugu da kari, wadannan tafiye-tafiye da yadda Sinawa ke murna, ya nuna cewa, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen ganin al’ummarta na rayuwa cikin jin dadi da aminci da wadata kuma cike da tsaro.(Fa'iza Mustapha)