An mika lambar yabo ta Nobel ta fannin magunguna ga Katalin Kariko da Drew Weissman
2023-10-03 20:15:35 CMG
A jiya ne cibiyar Karolinska ta kasar Sweden ta sanar da mika lambar yabo ta Nobel ta fannin magunguna ga Katalin Kariko da Drew Weissman, sabo da gaggarumar nasarar da suka cimma a fannin nazarin mRNA, nasarar da ta taimaka wajen gaggauta aikin nazarin alluran rigakafin Covid-19.