logo

HAUSA

An kaddamar da bikin baje-kolin lambuna na kasa da kasa a kasar Qatar

2023-10-03 16:12:17 CMG Hausa

An kaddamar da bikin baje-kolin lambunan kasa da kasa a Doha, fadar mulkin kasar Qatar, inda sarkin kasar, Tamim Bin Hamad Al Thani ya jagoranci kaddamar da shi a jiya Litinin.

Babban taken bikin na bana shi ne, “kiyaye muhallin hamada, da kiyaye muhallin halittu”, wanda ke kokarin karfafa gwiwar kasa da kasa don su lalibo sabbin hanyoyin magance kwararar hamada, da jan hankalin al’umma kan muhimmancin kiyaye muhalli, da daukar matakan zahiri a wannan fanni.

A jawabin da ya gabatar, firaministan kasar Qatar, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al Thani, ya yi kira ga kasa da kasa da su dauki matakai don kiyaye muhallin halittu, musamman ga zuriyoyin dake tafe, tare da inganta hadin-gwiwar kasashe daban-daban don cimma wannan babban buri. Rahotannin sun ruwaito cewa, za’a gudanar da bikin baje-kolin lambunan kasa da kasa na bana har zuwa ranar 28 ga watan Maris din shekara mai kamawa, wanda ya kasance karo na farko da aka shirya irin wannan bikin baje-koli dake da matsayi mafi girma na A1, a yankunan Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka. (Murtala Zhang)