logo

HAUSA

Daga yau Litinin `yan Najeriya sun kammala bukukuwan bikin cikar kasar shekaru 63 da samun `yanci.

2023-10-02 16:34:59 CMG Hausa

Yau Litinin 2 ga watan Oktoban ta kasance rana ta karshe da mahukunta a Najeriya suka ware domin bukukuwan bikin cikar kasar shekaru 63 da samun `yanci daga Turawan mulkin mallaka, gwamnati ta ware yau Litinin a matsayin ranar hutu a duk fadin kasar.

A jiya Lahadi shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga al`ummar kasar ta kafofin yada labarai, wanda hakan ke daga cikin tsare-tsaren bikin na bana.

Wakilin mu dake Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya saurari jawabin na shugaban kasa, ga kuma kadan daga cikin abubuwan da ya tsakuro mana.

Jawabin na shugaban kasa mai sakin layi 32 ya mayar da hankalin ne kan yanayin da ya tsinci kasar da kuma kokarin da gwamnatin sa ke yi wajen fito da kasar daga halin data shiga na koma bayan tattalin arziki, tabarbarewar tsaro, rashin aikin yi da kuma sha`anin yaki da cin hanci da rashawa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yace nan bada jimawa ba zai karbi rahoton kwamatin da ya kafa don nazari da binciken matsalolin da suka dabaibaye babban bankin kasar, yayin da kuma ya sanar da cewa ya kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji don inganta harkokin tara kudin shiga.

Ta fuskar samar da aikin yi kuwa, shugaba Tinubu ya ce tuni ya samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da suka nuna alamar makoma ta gari, baya ga samar da Karin jari ga kanana da matsakantan masana`antu da gwamnatin ta yi.

A kan batun sha`anin tsaro kuwa shugaban na tarayyar Najeriya yace gwamnati ta kyautata tsarin hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro, an kuma  karawa hafsoshin sojin kasar kaimi wajen farfado da karsashin rundunonin su, tare kuma da alkawari samar da wadatattun kayan aiki ga dakarun kasar.

Shugaba Tinubu ya cigaba da cewa. “Mun samar da wata sabuwar hanyar sufuri a kasa, a inda zamu bunkasa sha`anin hada-hadar gas na CNG mai saukin gaske da kuma rashin hatsari, bada jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa Gas za su fara isowa Najeriya, kuma za`a kafa cibiyoyin bada horo a fadin kasar domin koyarwa da bada sabbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana`antu kan hanyoyin karkata ga amfani da sabon makamashin gas na CNG, hakika samar da wannan sauyi kafa sabon tarihi ne”

Daga karshe shugaban na tarayyar Najeriya ya yiwa al`ummar kasar alkawarin cewa zai himmatu sosai wajen yi musu hidima ba tare da cin amanar kowa ba, kuma yana bukatar shawarwarin kowanne dan kasa.(Garba Abdullahi Bagwai)