logo

HAUSA

'Yar kasar Uzbekistan Gilly: Shugaban kasar Sin ya yanke shawarwari da dama wadanda suke da amfani ga ci gaban duniya

2023-10-02 20:11:12 CMG Hausa

Gilly, wadda ke koyar da harshen Uzbekistan a cibiyar koyon harsunan waje a jami'ar Minzu ta kasar Sin, ta shafe shekaru 13 tana kasar Sin. Daga Jami'ar horar da malaman makaranta ta Shaanxi zuwa Jami'ar Minzu ta kasar Sin, ta ce tana matukar godiya ga jami'o'in kasar Sin da dama da suka ba ta horo.

“Na yi karatu a jami’o’i da dama a kasar Sin, hakan na nufin makarantu da yawa suka yaye ni a kasar Sin. Sinanci ya samu karbuwa sosai a Uzbekistan a yayin da nake karatu a jami'a, shi ya sa ni ma kamar matasa da yawa a kasarmu na zabi koyon wannan harshe, daga baya Sinanci ya zama abin sha'awata.”

Gilly a ko da yaushe tana himmatuwa wajen ba wa kasarta ta Uzbekistan labaran kasar Sin, kuma ta shiga cikin ayyukan fassara wasu litattafan kasar Sin da dama da ayyukan gyara fassara zuwa harshen Uzbekistan tare da Gulibanumu, malamar dake koyar da harshen Uzbekistan ta jami'ar Minzu ta kasar Sin.

Gilly ta ce, a lokacin da ta halarci ayyukan fassara da gyarar fassaran  littafi mai taken "Labarun da Xi Jinping ya bayar", ta ji cewa, jawabai da labaran da shugaba Xi Jinping ya yi na da wani irin karfin shiga zukatan mutane. Ta ce,

“Wannan littafi yana da ban sha'awa, shugaba Xi yana amfani da hanyar ba da labari don sanar da wasu abubuwa masu ma'ana sosai, wadanda ke iya burge mutane.”

A cewar Gilly, shugaba Xi ya yi nuni da hanyar samun bunkasuwa ta "ganin tsaunuka, da ganin ruwa, da kuma tunawa da gari" kan ayyukan gine-ginen yankunan karkara na kasar Sin. Gaskiya, bayan shekaru masu yawa da ta yi zama a kasar Sin, ta ga cewa, ba wai kawai gwamnatin kasar Sin ta taimaka wa mutanen karkara su fita daga kangin talauci ba, har ma ta yi kokari sosai wajen kiyaye muhalli.

Gilly ba wai kawai ta shiga aikin gyara fassarar littafin "Xi Jinping ya ba da labarai" zuwa harshen Uzbekistan ba, har ma ta fassara littafin shugaba Xi Jinping mai suna "Kawar da kangin talauci". Ta ce, littafin "Kawar da kangin talauci" ya kunshi zurfin kaunar shugaba Xi Jinping ga jama'arsa da kuma kokarin da ‘yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke yi. Musamman ma wani babin dake cikinsa mai suna “Yaya za mu ba da ilmi yadda ya kamata” , wanda ya burge ta kwarai da gaske.

“Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, dole ne mu yi tunani kan batutuwan da suka shafi ilimi ta fuskar raya tattalin arziki da zamantakewa. A matsayina na ma'aikaciya a fannin ba da ilimi, irin ra’ayi na shugaba Xi ya burge ni sosai.”

A matsayinta na malama, Gilly ta ce, ci gaba da sauye-sauyen da ake samu a fannin ba da ilmi na tushe na kasar Sin, na da matukar muhimmanci ga kasar Uzbekistan.

“Na karanta litattafai da yawa game da tsarin ilimin kasar Sin. Har ila yau, mun fassara littafin "hanyar kasar Sin ta bunkasa aikin ba da ilimi na tushe", kuma a lokacin da ake aikin fassara wannan littafi ne na fito da wani tunanin yin nazari kan dalilan ci gaban ilimi a kasar Sin. Na yarda sosai da ra'ayin da shugaba Xi Jinping ya gabatar na 'kara mai da hankali sosai kan aikin ba da ilimi wanda ke kasancewar babban tushen kawar da talauci da samun wadata'. A kasarmu ta Uzbekistan, ana amfani da fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yin kwaskwarima ga tsarin ilimi. Yanzu, bisa ga tsarin ba da ilimin jama'a a Uzbekistan, malamai suna amfani da wannan littafi a matsayin jagora don nazarin dalilan da suka sa dalibai a makarantun Shanghai suka sami matsayi mafi girma a cikin shirye-shiryen tantance dalibai na duniya.”

A cikin aikin fassara da nazarin ayyukan shugaban kasar Sin, da lura da yadda kasar Sin ta samu ci gaba, da kuma yin tunani kan manufofin kasar Sin, Gilly ta yi matukar sha'awar ilmin da shugaban kasar Sin ya samu da hangen nesa da yake da shi.

“Shugaba Xi Jinping shugaba ne mai kwarjini da kyawawan halaye na babbar kasa. A cikin jawabansa, ko da yaushe yana iya yin amfani da ra'ayoyin adabin kasar Sin da ra'ayoyin falsafa wajen bayyana kowane irin ra'ayi, wanda ke nuna cewa yana da masaniya, kuma ya kware a fannin al'adu da tarihi, ta yadda zai iya yanke shawarwari da dama da suke da amfani ga ci gaban duniya.”

Don kara fahimtar kasar Sin, Gilly ta fassara ayyukan kasar Sin da dama, ta yi imanin cewa, ko a fannin dabarun mulkin kasar Sin ko kuma a fannin manufofin harkokin waje da kasar take bi, dukkansu Sinawa ke nuna kwarewarsu wajen fito da ma'ana daga kyawawan al'adu da ra'ayoyin kasar na gargajiya.

“Ma'anar falsafa da al'adun akida na Confucius su ne tagar fahimtar kasar Sin ta zamani. Ka'idar 'kimar daidaito' a kasar Sin ita ce manufar aiwatarwa a fannin da’a da ra’ayin Confucius ya gabatar. Confucius ya ce a cikin littafi mai taken ‘Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius’, cewa ‘zaman jituwa shi ne abu mafi daraja’. Dangantaka mai jituwa tare da yanayin zamantakewar jama'a mai kyau suna da mahimmanci ga rayuwar dan Adam da ci gaban kasa.”

Gilly ta kara da cewa, har ila yau Confucius ya gabatar da kafa kyakkyawar al'umma irin ta 'dukkan jama’a ke mallakar duniya', wanda ba wai kawai babban ra'ayin al'ummar kasar Sin a zamanin da ba ne, da kuma hikimar al'adun gargajiyar kasar Sin ba, har ma ya yi bayani kan ‘gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam’.

Gilly na fatan cewa, a nan gaba, Sin da Uzbekistan za su ci gaba da rubuta wani babi mai haske game da aikin raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa.

“Dangantakar da ke tsakanin Sin da Uzbekistan tana da dadadden tarihi, tun da dadewa, tare da hadin gwiwa sun zana hanyar siliki ta samu ci gaba mai cike da albarka tare da mu'amalar tattalin arziki da cinikayya da hadewar al'adu. A nan gaba, ina fatan kasashen biyu za su iya bude wani sabon babi na mu'amalar al'adu, da cudanya tsakanin jama'a, da kuma fahimtar juna tsakanin al'ummominsu.”