logo

HAUSA

Türkiye ta kaddamar da luguden wuta kan mayakan PKK a arewacin Iraqi

2023-10-02 17:56:37 CMG

Ma’aikatar kula da harkokin tsaro ta Türkiye, ta ce dakarun kasar sun kaddamar da luguden wuta a arewacin Iraqi tare da lalata wasu wurare 20 mallakin kungiyar mayakan Kurdawa ta PKK.

Matakin sojin na zuwa ne bayan wasu mahara biyu sun yi yunkurin tada bam a gaban ginin ma’aikatar harkokin cikin gidan Türkiye dake birnin Ankara da safiyar jiya Lahadi, lamarin da ya yi sanadin raunata wasu ‘yan sanda biyu

Daya daga cikin maharan ya mutu bayan tayar da bam na kunar bakin wake, yayin da ‘yan sanda suka harbe dayan har lahira.

Ma’aikatar harkokin gidan Türkiye ta ce an gano daya daga cikin maharan dan kungiyar mayakan Kurdawa na PKK ne, kuma tuni aka kaddamar da bincike domin gano asalin daya maharin. (Fa’iza Mustapha)