logo

HAUSA

Kasar Sin ta zama abar koyi ga goyon-bayan hadin-gwiwar kasashe masu tasowa

2023-10-02 17:15:52 CMG Hausa

Babbar darektar ofishin kula da harkokin hadin-gwiwar kasashe masu tasowa na Majalisar Dinkin Duniya, Madam Dima Al-Khatib ta bayyana cewa, kasar Sin na samar da cikakken goyon-baya ga hadin-gwiwar kasashe masu tasowa, da irin wadda ke kunshe da bangarori uku, haka kuma tana samun babbar nasara a fannin kawar da kangin talauci, al’amarin da ya zama abun misali ga kasashe daban-daban.

A gun babban taron shaida nasarorin hadin-gwiwa da suka shafi shawarar samar da ci gaba ga duniya da kasar Sin ta shirya, yayin muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da aka yi a hedikwatar majalisar dake birnin New York, Dima Al-Khatib ta gabatar da jawabin dake cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya duk duniya mai dorewa, bisa shawarar samar da ci gaba ga duniya.

Jami’ar ta kara da cewa, shawarar samar da ci gaba ga duniya da kasar Sin ta bullo da ita, za ta bayar da babbar gudummawa ga cimma buri iri daya na daukacin dan Adam, da kirkiro makoma mai dorewa da adalci da wadata. Kana, kasashe daban-daban, musamman kasashe masu tasowa, sun yaba sosai da gudummawar da kasar Sin ta bayar ga inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. (Murtala Zhang)