logo

HAUSA

An gudanar da bikin murnar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin karo na 74 a birnin Legos

2023-10-01 16:36:00 CMG Hausa

Kasar Sin ta bukaci Karin samun hadin kai tsakanin ta da Najeriya a bangarorin cinikayya da al`adu da kuma zamantakewa.

Karamar jakadar  kasar Sin a birnin Legos dake kudancin Najeriya Ms. Yan Yuqing ce ta bukaci hakan yayin bikin murnar cika shekaru 74 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, tace hadin kan kasashen biyu zai tabbatar da kyakkyawan fatan da ake da shi na samun cigaba mai ma`ana ta fuskoki da dama.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Madam Yan Yuqing ta ce irin gwagwarmayar da Najeriya ta yi da `yan mulkin mallaka kafin ta samu `yancin kai suna da kamanceceniya da fafutukar da `yan kasar Sin suka yi gabannin kasancewar kasar ginanniyar Jamhuriya.

Inda ta kara da cewa hakika, yana da mutukar alfanu kasashen biyu su cigaba da daukar tsare-tsaren da za su kara daga matsayin abokantakar su zuwa sabon matsayi.

“ Najeriya kasa ce mai dadadden tarihi na dubban shekaru kamar yadda kasar Sin take, kuma ta yi shuhura wajen wanzuwar al`adu daban daban, wannan ce ta ba ta damar kasancewa taga ga al`adun Afrika”

A nata jawabin, sakatariyar gwamnatin jihar Legos Mrs Bimbola Saluhudeen alkawari ta yi na cewa jihar Legas zata cigaba da kyautata alakar ta da kasar China ta yadda bangarorin biyu za su jima suna cin moriyar juna.

“Jihar legos, ta kasance zango na farko da duk wani mai saka jari ke muradin kwance hajar sa, muna da yawan al`umma, hakika a shirye muke mu hada karfi da gwamnatin  kasar China don tabbbar da ganin cewa gwamnatin jihar Legos ta kai ga nasarar burin da take son cimmawa.”

Jami`an gwamnati da dama ne suka halarci bikin, ciki har da karamin ministan tama da karafa na tarayyar Nijeriya Alhaji Uba Amadu wanda ya wakilci mataimakin shugaban kasa,inda a wannan lokaci ne ma ya bayyana irin cigaban da Najeriya ta samu tun bayan kulla hulda da kasar Sin sama da shekaru 50.

A karshe an gudanar da raye-rayen al`adu daban-daban na kasar Sin da Najeriya.(Garba Abdullahi Bagwai)