logo

HAUSA

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya ya shirya bikin murnar cikar Sin shekaru 74 da kafuwa

2023-10-01 17:05:39 CMG Hausa

A kwanan nan ne, ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen waje da dama, suka gudanar da bukukuwa iri-iri, domin murnar cika shekaru 74, da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.

A wajen irin wannan bikin da ofishin jakadancin Sin dake tarayyar Najeriya ya shirya, jakadan Sin a kasar Cui Jianchun, ya yi waiwaye game da yadda Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ta samu ci gaba, da nasarori a shekaru 74 da suka gabata, inda ya jaddada cewa, tun bayan da kasashen biyu suka kulla alakar jakadanci a shekara ta 1971, musamman bayan da suka daga matsayin alakar su, zuwa alakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a shekara ta 2005, ya zuwa yanzu, hadin-gwiwarsu na kan gaba sosai.

Jakada Cui ya kara da cewa, kasar Sin na fatan yin amfani da damar gudanar da babban dandalin tattauna hadin-gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku, gami da dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC a takaice, domin taimakawa ci gaban manufar raya Sin da Najeriya, wadda ake kira 5GIST, da kara habaka hadin-gwiwarsu.

Shi ma a nasa jawabin, mataimakin kakakin majalisar wakilan tarayyar Najeriya Benjamin Kalu, ya taya Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin murnar cika shekaru 74 da kafuwa, inda a cewarsa, Sin babbar aminiyar hadin-gwiwa ce ga Najeriya, kuma kasashen biyu sun cimma tudun-dafawa, wajen karfafa hadin-gwiwa, a fannonin da suka shafi samar da muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kasuwanci, da musanyar fasahohi, da al’adu da sauransu, al’amarin da ya taimaka matuka ga ci gaban rayuwar al’umma, gami da bunkasar tattalin arzikin Najeriya, da samar mata da dimbin guraban ayyukan yi, da taimakawa ci gaban sana’o’i daban-daban.

Jami’in ya ce, kasar Sin ta dade da yin kira, da a aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da samar da ci gaba mai dorewa kuma cikin lumana, kana ta taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya.

Daga nan sai ya bayyana fatansa, ga fadadar zumuncin kasashen biyu, da kara samar da damammaki, da alfanu ga al’ummunsu baki daya, da bayar da gudummawa ga shimfida zaman lafiya, da ci gaba a duk fadin duniya. (Murtala Zhang)