Majalissar dattijan Amurka ta amince da kudurin kasafin kudi da zai dakile tsayar da ayyukan gwamnati
2023-10-01 16:59:37 CMG
A daren jiya Asabar ne majalissar dattijan Amurka, ta amince da wani kuduri na samar da kwarya kwaryar kasafi, wanda zai hana tsayar da ayyukan gwamnatin kasar. Kasafin dai zai ba da damar gudanar da ayyukan gwamnati har tsawon kwanaki 45, ya kuma zo a gabar da gwamnatin Amurkar ke daf da shiga hali na dakatar da ayyuka.
An dai kada kuri’un amincewa da matakan samar da kudaden ne a zauren majalissar dattawan Amurka a jiyan, inda ‘yan majalissa 88 suka amince da matakan, yayin da 9 suka kada kuri’un kin amincewa. Kaza lika kafin hakan, sai da ‘yan majalissar wakilan kasar suka kada kuri’un amincewa da kudurin, da kuri’u 335, yayin da wasu 91 suka ki amincewa.
Da safiyar jiya Asabar din ne kakakin majalissar wakilan kasar Kevin McCarthy, wanda ya sha fama kafin shawo kan ‘yan majalissar masu tsattsauran ra’ayi daga jami’iyyar Republican game da amincewa da kudurin, ya shelanta shirin, wanda zai baiwa hukumomin gwamnatin tarayyar kasar damar ci gaba da samun kudaden gudanarwa, bisa matsayin da ake ciki yanzu, har ya zuwa tsakiyar watan Nuwamba, ciki har da dalar Amurka biliyan 16 ta ayyukan shawo kan bala’u.
Sabon kudurin dai ya ki amincewa da matakin matse bakin aljihu da masu ra’ayin rikau daga jam’iyyar Republican suka nema, a hannu guda kuma bai kunshi tanadin karin wani tallafi ga kasar Ukraine da ‘yan jami’iyyar Democrats suka nema ba.
Tun a jiyan ne kuma shugaban Amurka Joe Biden, ya rattaba hannu kan kudurin, kuma da hakan gwamnatin Amurka ta kaucewa fadawa yanayi na dakatar da ayyuka, kamar dai yadda fadar White House ta tabbatar. (Saminu Alhassan)