logo

HAUSA

Kasashen Sin da Amurka sun yi shawarwari kan harkokin yankin Asiya da tekun Pasifik a birnin Washington

2023-09-30 17:00:39 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana cewa, manyan jami’an diflomasiyyar Sin da Amurka sun yi musayar ra’ayi na hakika tare da zurfafa ma’ana, game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da yanayin yankin Asiya da tekun Pasifik, da manufofin shiyya-shiyya, da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu duka.

A cikin wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar a jiya Juma’a, ta ce, mataimakin ministan harkokin wajen Sin Sun Weidong, bisa fahimtar juna da bangarorin biyu suka yi, da kuma gayyatar da bangaren Amurka ya yi masa, ya gabatar da shawarwari kan harkokin Asiya da tekun Pasifik tare da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasifik wato Daniel Kritenbrink a birnin Washington na kasar Amurka a ranar Laraba.

Sun ya bayyana matsayin kasar Sin game da batun Taiwan, ya kuma jaddada cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce ginshikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan.

Ya kuma bayyana matsayin kasar Sin kan abin da ake kira "Dabarun Indo-Pacific" na Amurka da kuma kan tekun kudancin kasar Sin.

Bangaren kasar Sin ya jaddada cewa, kyakkyawar mu'amalar da ke tsakanin Sin da Amurka a yankin Asiya da tekun Pasifik ta dace da moriyar kasashen biyu, da kuma cimma burin da kasashen yankin suke da shi, a cewar sanarwar. Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa kan harkokin Asiya da tekun Pasific. (Yahaya)