logo

HAUSA

Masu kanana da matsakaitan masana'antu a Najeriya zasu fara shiga duniyar kasuwanci ta hanyar fasahar zamani

2023-09-30 16:23:07 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da shirin dabarun bunkasar kasuwanci ta hanyar fasahar zamani wanda a kalla masu kananan da matsakaitan sana’o’i miliyan 3 za su ci gajiya.

A lokacin da ya kaddamar da shirin jiya juma’a a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yace yanzu an shiga yanayi na juyin juya halin kasuwanci ta fasahar zamani a duniya wanda kuma bai kamata a bar Najeriya a baya ba.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shirin mai taken DIGITAL SKILLNOVATION za a tafiyar da shi ne bisa hadin gwiwa da bankunan kasuwancin kasar, kuma zai baiwa masu kanana da matsakantan masana`antu damar samun bayanai akan yadda zasu fadada harkokinsu a duniya baki daya ta fuskar mu`amullar tattalin arziki da zamatakewa tare da habaka cigaban samar da kayayyaki a Najeriya.

Karkashin wannan shiri, za a samar da cibiyoyi na fasahar sadarwar zamani guda 15 a sassa daban daban domin baiwa daidaikun mutane da `yan kasuwa damar samun horo a kan amfani da fasahohin zamani, da samar masu da kayan aiki, kana da sauran agajin da aka tabbatar zai yi tasiri ga harkokin kasuwancin su a zamanance.

“Mun himmatu wajen tabbatar da ganin ba’a bar kowa a baya ba a fafutukar wayar da kai game da sha`anin fasahar zamani, yanzu haka Najeriya na samun karuwar kanana da matsakaitan masana`antu a sassa daban-daban wanda a halin yanzu adadin su ya kai miliyan 40, wanda wannan ya isa ace suna jagoracin sabbin dabarun kasuwanci ta fasahar zamani a  nahiyar Afrika baki daya, manufar dai samar da wannan shiri shi ne domin a bude wannan babbar dama da aka samu domin `yan kasuwar mu su rinka cin gajiya, kuma karkashin wannan shiri an tsara samar da dukkan wani nau’in horo da kuma kayan aiki da suka kamata don tabbatar da ganin cewa, masu kanana da matsakaitan sana’o’i a Najeriya sun bunkasa tare kuma da ganin ana gogayya da su a duniya baki daya.”

Kashin farko na shirin zai mayar da hankali ne a jahohin Katsina, Anambra, Borno, Legos da kuma Kano. Yayin da kuma kashi na biyu zai nufi jahohin Delta, Kaduna, Ogun, Bauchi da Ekiti.(Garba Abdullahi Bagwai)