logo

HAUSA

Babban dan majalisar dokokin Sin ya halarci taron majalisar dakokin BRICS karo na 9

2023-09-30 16:51:41 CMG Hausa

Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, ya halarci taron majalisar dokokin BRICS karo na 9, wanda aka gudanar a birnin Johannesburg ta Afirka ta Kudu daga ranar Laraba zuwa Alhamis, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.

Peng ya ce, kasashen BRICS sun zama wani muhimmin jigo wajen daidaita yanayin kasa da kasa. Ya yi fatan kasashen BRICS za su ba da himma sosai ga shirin raya kasa da kasa, da shirin samar da tsaro a duniya, da shirin wayewar kai da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar don inganta zaman lafiya da ci gaban duniya.

Har ila yau, ya bukaci majalisun dokokin kasashen BRICS da su aiwatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin BRICS karo na 15, da daukar ci gaban BRICS a matsayin wata dama, da karfafa gina tsarin dandalin majalisar dokokin BRICS, da yin mu'amala ta hanyoyi da dama a tsakanin majalisun dokokin kungiyar, da kuma taimaka wa sababbin membobi shiga cikin hadin gwiwar majalisar dokokin BRICS da wuri-wuri. (Yahaya)