logo

HAUSA

Guterres ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a Pakistan

2023-09-30 17:04:37 CMG

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci guda biyu da aka kai jiya Jumma'a a kasar Pakistan.

Guterres ya bayyana ta hannun kakakinsa, Stephane Dujarric cewa, “muna matukar yin Allah wadai da hare-haren ta'addancin da aka kai a kasar Pakistan, wadanda suka halaka mutane fiye da 50. Yana mai cewa, akwai bukatar a hukunta wadanda ke da hannu a wannan danyen aiki”

Jami'an 'yan sandan da na kiwon lafiya a kasar Pakistan, sun ce wata fashewa da ta afku a wani taron addini a yankin Mastung na lardin Balochistan da ke kudu maso yammacin kasar Pakistan a ranar Juma'a, ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50 tare da jikkata wasu akalla 50. Fashewar wadda ake kyautata zaton harin kunar bakin wake ne, ta afku ne a kusa da wani masallaci a lokacin da jama'a suke taruwa domin yin bikin Maulidi, wato murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad(SAW)

A wani hari na daban da aka kai a jiyan, mutane 5 ne suka mutu, wasu 10 kuma suka jikkata, bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai a cikin wani masallaci a lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin kasar. (Ibrahim)