logo

HAUSA

Me kuka sani game da bikin haduwa da iyali na Sinawa

2023-09-29 17:49:14 CRI

Bikin Zhongqiu na daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya na kasar Sin, wato ya fado a daidai tsakiyar yanayin kaka, shi ya sa ake kiransa bikin Zhongqiu, wato bikin tsakiyar yanayin kaka. Kuma a wannan shekara, ya fado ne a yau Jumma'a 20 ga wata. A wannan rana, wata ya kan cika fal, kuma a lokacin da jama’a ke hango duniyar wata, su kan fara kewan iyalansu, shi ya sa Sinawa suke kuma daukar bikin a matsayin bikin haduwar iyali. 

A biyo mu cikin shirin, don jin karin haske.