logo

HAUSA

Masana kimiyya na Sin da Afrika sun lashi takobin hada gwiwa wajen ganin an cimma ajandar kyautata rayuwar jama’a

2023-09-28 09:57:44 CMG Hausa

Masana kimiyya daga kasashen Sin da Afrika, sun lashi takobin kara hada gwiwa domin cimma wasu manufofin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, ciki har da wadatar abinci da kare muhallin halittu.

Cikin kudurorin da suka dauka a karshen taron karawa juna sani da suka yi a Nairobin Kenya, masanan sun jadadda cewa, hadin gwiwa a muhimman fannoni kamar na bincike da musayar fasahohi da inganta dabaru, na da muhimmanci wajen samar da kyakkyawan sauyi a kasashe da bunkasa tsarin kare muhalli.

Masanan Sin da Afrika kusan 100 ne suka halarci taron da ya gudana daga ranar 25 zuwa 27 ga wata, wanda aka yi wa taken, “Hadin gwiwar kasashe masu tasowa: Hadin gwiwar Sin da Afrika kan kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire domin amfanawa al’umma da tattalin arzikin”.

Shirin kawancen raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasashen Afrika na hukumar raya kasashe ta kungiyar Tarayyar Afrika AUDA-NEPAD, da kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin (CAS) da ofishin tawagar Sin a AU ne suka shirya taron na kwanaki 3. Wasu daga cikin mahalarta taron da suka fito daga sassan gwamnatoci da cibiyoyin bincike na Sin da na Afrika, sun tattauna kan inganta hadin gwiwa a muhimman bangarori 3 da suka hada da sauya tsarin samar da abinci da kare mabambantan halittu da kuma tsimin ruwa. (Fa’iza Mustapha)