logo

HAUSA

Cibiyar kimiyyar noma na Sin CATAS ta cancanci yabo

2023-09-28 16:54:45 CMG Hausa

Kasar Congo Brazzaville wadda ke yankin tsakiyar Afirka, na da albarkatun noma baya ga danyen mai, kuma ’yan kasar na alfahari, da cin gajiya daga sana’ar noma, to amma aikin noma a wannan zamani na bukatar kwarewa, sanin makamar aiki, da amfani da fasahohin zamani domin samun cikakkiyar gajiya.

Bisa hakan ne ma cibiyar kimiya ta bunkasa noma a yankuna masu zafi ta kasar Sin ko CATAS, ta kuduri aniyar horas da manoma da jami’ai a Congo, dabarun amfani da na’urorin zamani na inganta wannan sana’a. A baya bayan nan, jami’an wannan cibiya ta CATAS sun gudanar da irin wannan horo a birnin Haikou, fadar mulkin lardin Hainan na kasar Sin. Kazalika wasu jami’an cibiyar ta CATAS sun gabatarwa daliban Congo dabarun kimiyya na bunkasa noma a wasu gonakin dake kusa da birnin Brazzaville, fadar mulkin kasar ta Congo.

A cikin shekaru biyar, kwararru daga CATAS dake aiki a Brazzaville, suka gudanar da horaswa har sau 29, inda suka gabatarwa manoman kasar, da jami’an sashen noma dabaru daban daban na wanzar da ci gaban sana’ar noma a kasar.

Ko shakka babu, kwararru a wannan muhimmin fanni na noma daga kasar Sin, sun shuka wata muhimmiyar alaka ta inganta noma, musamman a yankunan wannan kasa mai dumi dake tsakiyar Afirka, wanda hakan ya sanya dan ba ga inganta hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka.

Karkashin kwazon wadannan kwararru na cibiyar CATAS, an tura sama da rukunin masana 20 zuwa Congo, domin su gudanar da tallafin horaswa na inganta fasahar noma, suna kuma ci gaba da aiki a cibiyar gwaji ta “ATDC” tun daga shekarar 2007 kawo yanzu.

Ana iya ganin tasirin wannan muhimmin aiki a Congo, inda manoman wurin ke gwada sabbin iri na yanayin zafi, da noman kaji, da sauran sassan bunkasa noma.

Tabbas, a sana’ar noma, samun kwarewa, ta amfani da kimiyya da fasahohin zamani, jigo ne na cimma nasarar da ake fata. A wannan gaba da Congo Brazzaville ke more fasahohin kwararru daga kasar Sin, muna iya cewa hakan abun a yaba ne, kuma yana kara nuna aniyar kasar Sin ta yada fasahohinta na ci gaba, ga sauran kasashe masu tasowa dake nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)