logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a sanya batun Falesdinu kan gaba cikin jadawalin tattaunawar kasa da kasa

2023-09-28 14:41:22 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya yi kira da a inganta aikin neman sulhu, da ciyar da “daftarin kasashe biyu” gaba, tare da sanya batun Falesdinu kan gaba cikin jadawalin tattaunawa tsakanin kasashen duniya.

A yayin taron tattaunawa kan batun Falesdinu na yankin Gabas ta Tsakiya na kwamitin sulhu na MDD, Geng Shuang ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana ci gaba da fama da tashe-tashen hankula a yankunan da aka mamaye a Falesdinu. Shi ya sa, yanzu, ya kamata a tsaya tsayin daka kan aniyar siyasa, da daukar matakai masu amfani, da kuma hadin kai, domin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)