logo

HAUSA

Dakarun sojin saman Najeriya sun samu nasarar tarwatsa maboyar ’yan kungiyar tsagerun IPOB da ESN

2023-09-28 09:47:38 CMG Hausa

Rundunar tsaron sojin sama ta Najeriya ta kai jerin hare-hare ta sama sansanonin kungiyar IPOB da dakarun ’yan awaren ESN masu fafutukar raba Najeriya a yankin kananan hukumomin Nnewi ta kudu dake jihar Anambra da kuma Okigwe a jihar Imo.

Kamar yadda rundunar ta fada, ta ce harin na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi ne na kawo karshen ayyukan kungiyoyin a yankin wadanda suka jima suna yin ta’adi ga kaddarorin gwamnati tare kuma da barazana ga rayukan jama’a a yankunan kudu maso gabashin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kamar yadda darektan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar Air Kwamandor Edward Gabkwet ya shaidawa manema labarai jiya Laraba, ya ce, bayanan sirri da aka samu sun nuna cewa, kungiyar ta IPOB da kuma ta dakarun ’yan awaren ESN suna da wani shiri na aikata ta’addanci a yayin bukukuwan ranar samun ’yancin Najeriya a jihar Anambra da kuma sauran jihohin da suke a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Ya ce dai, an kai harin ne bisa hadin gwiwa da dakarun sojin kasa da kuma sauran hukumomin tsaro.

“An tabbatar cewa wadannan mutane sun riga sun shirya su kai hari ga sojojinmu da mutanen da suke tafiye-tafiyen kasuwanci, kuma sun tsara za su kai wadannan hare-hare daga yanzu zuwa daya ga watan Oktoba ranar samun ’yancin kan Najeriya, to, da aka ji wannan labari sai aka bayar da izinin a je a kai musu hari. Abun da ya faru ke nan aka kai musu hari a wani wurin da ake kira Orsumughu cikin jeji inda suke tara makamansu a jihar Anambra da wani wuri kuma ana kiransa Aku-Ihube a jihar Imo, an kai harin ranar Talata ne, bayan an gama da Anambra sai aka je jihar Imo kuma cikin ikon Allah an samu nasara, mu aikin mu shi ne Najeriya ta ci gaba da zama kasa daya, kuma ko waye daya ga kamar shi zai dinga tafiya din ta kashe mutane, ya hana su fita su je kasuwa, ba za mu bar wadannan mutanen ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)