logo

HAUSA

Damben Boxing: Zhang Zhilei na Sin ya doke Joe Joyce na Birtaniya a fafatawar su karo na 2

2023-09-28 20:19:58 CMG Hausa

Dan damben Boxing ajin masu nauyi daga kasar Sin Zhang Zhilei, ya doke abokin karawarsa Joe Joyce na birtaniya, a zagaye na 3 na fafatawar su a karshen mako, da kuma wannan nasara Zhang ya ci gaba da rike kambin da ya kwace a hannun Joyce.

Kafin wannan karo, a watan Afirilun bana, Zhang wanda ake yiwa lakabi da “Big Bang”, ya doke Joyce a zagaye na 6 na fafatawar da suka yi a Londan, a kuma wannan lokaci ne ya karbe kambin gasar hukumar shirya damben Boxing ta duniya WBO.

Kafin Zhang ya doke shi a wasan na watan Afirilu, Joyce ya jima yana rike da kambin WBO ajin masu nauyi, bayan doke shi da Zhang ya yi ne kuma ya nemi su sake karawa a wannan karo, wanda a wannan lokacin ma Zhang ya sake doke shi.

A wannan karo Joyce mai shekaru 38 da haihuwa, wanda a wannan karo ya zo da karin nauyi, ya sha naushi daga Zhang. Ya kuma fara gajiyawa tun a zagaye na 2 na fafatawar kafin daga karshe ya fadi kasa a zagaye na 3.

A cewar Zhang, "Joyce ya yi nauyi, amma hakan bai kara masa karfi ba, maimakon haka ya rage kuzari, da kyar yake daga kafafunsa".

Yanzu haka dai Zhang mai shekaru 40, yana harin karawa da dan damben Birtaniya Tyson Fury. Kafin ma karawarsa da Joyce a wannan karo, Zhang ya yi nufin karawa da Fury, har ma manajojinsa sun fara tuntubar Fury, kafin ba zato ba tsammani Joyce ya bayyana neman karawa da Zhang.

Tun dai kafin karawa da Joyce, Zhang ya isa birnin London, ya kuma rika bayyana kwarin gwiwarsa game da wasan da zai fafata da Joyce, har ma ya ce zai iya kawo karshen sana’ar damben Joyce. A cewar Zhang "Ba zan taba yin kuri ba, ina da kwarin gwiwa saboda na jima ina aiki tukuru, na kuma san zan iya cimma wannan nasara".

A baya can a shekarar 2008, Zhang ya lashe lambar azurfa a gasar dambe ta Olympic, kuma a yanzu yana da burin lashe babban kambun gasar ajin kwararru. Ya kuma ce wannan ne burin da ya jima yana fatan tabbatar sa, kuma mai yiwuwa ya cimma hakan a wasan sa na gaba.


Daga Pyeongchang zuwa Hangzhou burin aikin sa kai ya tabbata


Shekaru 5 da suka gabata, lokacin da matashiya Lee Kyong-min ke karatu a makarantar sakandare a Korea ta kudu, ta yi fatan zama daya daga cikin masu aikin sa kai yayin gasar Olympics ta lokacin hunturu da ta gudana a PyeongChang, amma a lokacin ba ta samu damar hakan ba saboda karancin shekarun ta. A yanzu haka tana da shekaru 22 a duniya, kuma mafarkin ta ya tabbata a gasar wasanni ta Asiya dake gudana a birnin Hangzhou.

Lee, wadda ‘yar asalin birnin Seoul ce, ta kulla hulda da kasar Sin ne lokacin da ta fara koyon darashin Sinanci a makarantar sakandare. A cewar ta, "Lokacin ina sakandare, na taba shiga rukunin masu koyon darussa yayin hutun bazara, inda muka zauna a birnin Beijing tsawon makwanni 2, a wannan lokacin ne kuma na fara zuwa kasar Sin, wadda ta burge ni matuka". Lee Kyong-min ta dandana gasasshiyar agwagwar Beijing, ta kuma ganewa idanun ta kayatattun gine gine masu halayyar musamman na Sin. A cewar ta, "Wadannan abubuwa sun sa ni kara sha’awar Sin, kuma abokai na Sinawa dake kewaye da ni sun taimaka min matuka, don haka sai na yanke shawarar yin karatu a Sin".

Kafin kammala karatun ta na sakandare, matashiyar tare da iyalan ta sun ziyarci biranen Shanghai da Hangzhou, kuma ziyartar su a tafkin yamma, da wurin ibada na Lingyin, da kyakkyawan muhallin birnin Hangzhou ya kara sanya ta jin sha’awar ta zauna. Ta ce "Daga lokacin na fara neman gurbin karatu a jami’ar Zhejiang. Na san wannan makaranta ce da ta shahara sosai a kasar Sin, kuma tabbas zan samu digiri mai nagarta a nan".

Bayan ta kammala karatun sakandare, Lee ta shafe tsawon shekara guda tana koyon Sinanci a Korea ta kudu. A shekarar 2020, Lee ta fara karatun digirin farko a fannin ilimin harkokin al’umma a jami’ar Zhejiang. Yayin da take rayuwa a birnin Hangzhou, Lee ta ji dadin kasancewa da mutanen birnin, saboda kaunar su ga baki, da kuma nau’o’in abinci masu dadi na mutanen wurin. Kaza lika, gudanar gasar wasanni ta asiya a birnin na Hangzhou ta kara mata jin dadin rayuwa a nesa da gida.

Lee ta ce "Lokacin da na shiga shekara ta 2 a jami’a, na sanya hannu domin shiga jerin masu ba da hidima ta sa kai, yayin gasar ta Hangzhou, kasancewar ban ji dadin rasa wannan dama yayin gasar Olympics ta PyeongChang ba. A wannan karo ina fatan cimma buri na, kuma iyaye na sun ba ni kwarin gwiwa yadda ya kamata".

Bayan shafe shekaru da dama tana shiri da samun horo, Lee ta zama mai aikin sa kai a fannin ba da hidimar fassahar harshe, a babbar cibiyar watsa labarai ta gasar wasannin Asiya dake gudana a birnin Hangzhou, inda ta fara aiki tun daga 9 ga watan Satumba, a fannin taimakawa masu daukar rahotanni na Korea ta kudu dake aiki a cibiyar.

Ta ce "Akwai ‘yan jarida da dama daga Korea ta kudu da suke aiki a yayin wannan gasa, kuma ina kokarin taimaka musu, wani lokacin ma ina fassara musu tambayoyi daga takwarorin su na Sin".

Lee na aiki a cibiyar a kullum tun daga 9 na safe zuwa 3:30 na yamma, kuma bayan nan sai ta koma makaranta dake da nisan kilomita 10 daga wurin, inda take karatu ta yanar gizo.

A cewar ta "Ina kaunar wasanni, kuma ina son kallon kwallo, kuma saboda kungiyar kasar mu tana da karfi sosai ina son na kalli wasannin ta, amma kasancewar ina aikin sa kai ba zan iya zuwa kallon wasan ba. Duk da ina jin ba dadi sakamakon haka, aikin da nake yi a cibiyar watsa labarai ya fi muhimmanci. Ina fatan taimakawa, ta yadda Sinawa da al’ummar Korea za su kara gano abubuwa da dama game da junan su. Duk da cewa aiki na ya shafi fannin ba da hidima ne kadai, ina ganin ta hakan, ‘yan jaridar Korea za su iya kara fahimtar Hangzhou, da Sin baki daya, suma kuma Sinawa za su kara fahimtar Korea ta kudu".

Kasancewar Lee ta ziyarci wasu biranen kasar Sin, kamar Nanjing da Qingdao, ta samu ganewa idanun ta ci gaban da kasar Sin ta samu. A kwanakin baya bayan nan, ta ji yadda ‘yan jaridar kasar ta ke yabon tsarin da aka yi na aiki a cibiyar watsa labarai ta gasar dake gudana.

Ta ce "Fata na shi ne samar da wata gada ta tattaunawa tsakanin Sin da Korea ta kudu, tare da fatan yin aiki a kamfanin cinikayyar waje na Korea bayan na kammala karatu, ta yadda zan ingiza hada hadar cinikayya tsakanin Sin da Korea ta kudu".