logo

HAUSA

An yi bikin ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a Habasha

2023-09-28 10:46:20 CMG Hausa

Al’ummar Sinawa mazauna kasar Habasha, ta yi bikin cika shekaru 74 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, wanda ke gudana a ranar 1 ga watan Oktoba.

Bikin wanda ya gudana a Addis Ababa, babban birnin Habasha, ya samu halartar wakilai daga kasashen Afrika daban-daban da manyan jami’an kungiyar Tarayyar Afrika (AU) da jami’an gwamnatin Habasha da jami’an diflomasiyya dake kasar da kuma wakilan al’ummun Sinawa dake Habasha.

Da take jawabi yayin bikin, mataimakiyar shugaban hukumar AU Monique Nsanzabaganwa, ta bayyana cewa, tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin shekaru 74 da suka gabata, kasar ta dauki hanyar neman farfadowa da kanta.

Ta ce Sin da nahiyar Afrika sun kulla zumunta mai karfi tare da gudanar da kyakkywan hadin gwiwa kan yaki da fatara, wanda ya zama misalin sabon tsarin inganta huldar kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)