logo

HAUSA

Jakadan Sin ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi kokari tare wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya

2023-09-27 11:13:43 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Geneva na kasar Switzerland, jakada Chen Xu, ya yi kira ga bangarori daban daban da su yi tattaunawa da juna bisa tushen adalci da girmama juna, da kara yin hadin gwiwa don tinkarar kalubale, a kokarin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.

Chen ya yi wannan furuci ne yayin da yake yin jawabi a gun taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 54 da aka yi a jiya. Inda Chen ya yi nuni da cewa, wasu kasashen yammacin duniya kamar Birtaniya da Amurka, suna fama da matsalolin nuna wariyar launin fata, da kyamar baki, da nuna wariyar addini, da talauci, da rashin aikin yi da sauransu. Amma wadannan kasashe sun rufe ido kan yadda suke take hakkin dan Adam, inda suke zargin kasashe masu tasowa a wannan fanni, yadda suke siyasantar da batun hakkin dan Adam, ba za su taba cimma nasara ba.

Chen ya kara da cewa, Sin ta gabatar da takardar bayani mai taken “Hada kai don gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama: Shawara da matakan Sin”, wadda ta yi bayani game da tunanin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, tare da jaddada cewa Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa cikin lumana, da himmatuwa wajen yin hadin gwiwa don samun nasara tare. (Zainab)