logo

HAUSA

CMG ta kaddamar da wani biki don fara nuna shirin “Journey Through Civilizations” a kasar Peru

2023-09-27 21:46:24 CMG Hausa

Jiya Talata 26 ga wata ne, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da wani biki don kaddamar da nune-nunen “Journey Through Civilizations” wato hanyar fahimtar wayewar kai a Lima, babban birnin kasar Peru.

Mataimakin shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong ya bayyana cewa, bikin nune-nunen nan da ake kira “Journey Through Civilizations”, ya shaida asalin “wayewar kai ta kasar Sin”, wanda shi ne wani kokari na daban da aka yi domin gano al’adun gargajiya na kasar. Mista Shen yana maraba da abokai da aminai don su halarci bikin, da yin musanyar al’adu tsakanin juna, domin samar da makoma mai haske ga ci gaban wayewar kai na daukacin al’umma. (Murtala Zhang)