logo

HAUSA

Jakadan Faransa a Nijar ya bar kasar

2023-09-27 19:38:41 CMG

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a safiyar yau Laraba ne jakadan Faransa a jamhuriyar Nijar Sylvain Itte ya fice daga kasar, kimanin wata guda bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba da umarnin korar shi daga kasar, a cewar majiya daga kasar Nijar da Faransa.

Wata majiya a ma’aikatar harkokin cikin gida ta Nijar ta tabbatar da tashin jirgin kuma ta ce ya nufi kasar Chadi.

Daga baya fadar shugaban kasar Faransa ya tabbatar da wannan rahoton. (Yahaya)