logo

HAUSA

Yadda kasashen Sin da Afirka ke neman Ci gaba tare karkashin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya

2023-09-27 09:46:35 CMG Hausa

Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani dalla-dalla game da manufar kasar Sin kan nahiyar Afrika a kasar Tanzania, wadda ta tsara makomar hadin gwiwar kasashen Sin da Afrika a sabon zamani, wannan alaka ta haifar da kawance da kulla dangantaka da yarda da juna tsakanin sassan biyu.

Wannan manufa mai tarin fa’ida da shugaba Xi ya gabatar, yayin ziyarar farko da ya kai a nahiyar Afrika, a matsayinsa na shugaban kasar Sin a shekarar 2013, ta dogaro ne bisa gaskiya da samun managartan sakamako da fahimtar juna.

Bisa wadannan tsare-tsare, kasashen Sin da Afrika, suka kasance tamkar ’yanuwa kuma abokai na kwarai, wajen samar da tafarkin samun ci gaba na bai daya, don samar da dangantaka mai karfi da ba a taba ganin irinta ba, tsakanin kasar dake nahiyar Asia da wadda ke nahiyar Afrika, wadanda yawan al'ummominsu ya kai biliyan 2.5, kwatankwacin daya bisa ukun al'ummar duniya baki daya.

Kuma ya zuwa wannan lokaci, duniya na iya ganin dimbin moriyar da aka samu bisa wannan dangantaka a fannoni da suka hada da tattalin arziki,da Ilimi, da cinikayya, da kayayyakin more rayuwa, da al’adu, da aikin noma,da raya masana’antu da kaiwa juna ziyara a bangare manyan jami’ai. Wani muhimmin batu da ya kara kyautata rayuwar al’ummomin sassan biyu a wannan alaka, ita ce shawarar ziri daya da hanya daya, shawarar da ta samar da ayyukan more rayuwa da zuba jari mafi girma a tarihi, wadanda suka taba rayuwar al’ummomi masu tarin yawa, musamman a kasashe masu tasowa da dama.

A yayin da shawarar ke cika shekaru goma cif da kafuwa, bayanai na nuna cewa, shawarar ta magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki ba ma a yankin nahiyar Afirka kawai ba, har da yankin Asiya da Fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)