logo

HAUSA

Sin tana son hada kai da bangarori daban daban don ciyar da shirin kawar da makaman nukiliya gaba

2023-09-27 14:05:46 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Geng Shuang ya bayyana a jiya cewa, Sin tana son yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, don ciyar da shirin kawar da makaman nukiliya gaba, ta yadda za a cimma burin kawar da makaman nukiliya a doron duniya cikin hanzari.

Geng Shuang ya bayyana a gun taron koli na MDD na tunawa da ranar kawar da makaman nukiliya na duniya cewa, makaman nukiliya babbar barazanar tsaro ce da dukkan kasashen duniya suke fuskanta, hana da kawar da makaman nukiliya daga dukkan fannoni a duniya shi ne burin dukkan dan Adam. Kasar Sin tana goyon bayan shawarar rage yawan makaman nukiliya, kana tana goyon bayan babban taron MDD wajen gudanar da taro domin tunawa da ranar kawar da makaman nukiliya na duniya, da kuma sa kaimi ga cimma wannan buri.

Geng Shuang ya kara da cewa, yayin da ake fuskantar kalubale da yanayi mai sarkakiya a duniya, ya kamata kasa da kasa su martaba ra’ayin bangarori daban daban, da kiyaye ka’idojin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, da sa kaimi ga shirin kwance damarar makaman nukiliya na kasa da kasa. (Zainab)