Kaiwa makura wajen rike numfashi yayin nutso cikin ruwa
2023-10-05 21:20:38 CRI
Tsawon wane lokaci ne mutum zai iya shafewa yana nutso a cikin ruwa ba tare da ya yi amfani da kayan taimakawa numfashi ba, iya rike numfashi ne kawai? Wannan tambaya ce mai muhimmanci da masu nutso cikin ruwa ke fatan samun amsar ta. Amma a bangaren ta, kwararriyar mai wasan nutso cikin ruwa ‘yar kasar Sin Xu Tongtong na ganin amsar ita ce "Wuce iyaka ".
Wasan nutso cikin ruwa ba tare da amfani da kayan taimakawa numfashi ba ko “Freediving” a turance, ya samo asali ne daga yankin Meditereniya, amma a yanzu ya zamo wasa da ya karade duniya baki daya. Masu wannan wasa na daidaita numfashin su ta hanyar sabarwa hunhun su rike numfashi na tsawon lokaci mai yawa. Wannan wasa na da bangarori guda biyu: Kaiwa wuri mai nisa da kuma sauri; wato wanda ya kai wuri mafi zurfi a ruwa budadde, ko ya yi linkaya cikin ruwa kebantacce shi ne ya yi nasara.
A cikin wannan shekara ta bana, Xu mai shekaru 35 da haihuwa, ta cimma nasarar yin nutson mitoci 100 a karkashin ruwa, a nau’o’in wasannin masu tabbataccen nauyi ko “CWT’, da na masu tabbataccen nauyi dake amfani da takalmin linkaya ko “bifin” wanda ake yiwa lakabi da “CWTB’, inda ta zamo ‘yar wasan linkaya mace ta 3 a duniya da ta cimma nasarar yin hakan.
Yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin larabai na Xinhua, Xu ta tuna nasarar da ta cimma, inda ta ce "Lokacin da na kai zurfin mita 100, na kuma dauko alamar da aka sanya, na san na cimma nasara. Na yi ninkaya zuwa saman ruwa cike da murmushi".
Kafin zama kwararriyar ‘yar wasan linkaya a shekarar 2014, Xu ‘yar asalin lardin Anhui na gabashin kasar Sin ce, a can ne kuma ta fara wasan nutso cikin ruwa, inda sannu a hankali ta samu sha’awar wasan yadda ya kamata. A cewar ta, "Babban nishadin wasan linkaya shi ne shawo kan tsoro. Horon da ake samu ya shafi mutum ya ci gaba da fahimtar kan sa. Duhu da rashin tabbas, su ne manyan dalilan da suke haifarwa dan adam tsoro, yayin da a nasa bangare, wasan nutso cikin ruwa ke kawarwa mutum wannan tsaro ta hanyar atisaye mai tushe daga kimiyya.
Kafin kaiwa ga nasara, Xu ta taba fuskantar matsala, ta yadda ta gaza ci gaba da kara nisan da take yi a kasan ruwa saboda tsoron zurfi. Amma daga baya ta ce ta shawo kan wannan tsoro, har ta kai matsayin da ba ta jin tsoron wani abu game da nutso cikin ruwa.
Bayan ta shafe watanni 3 cikin shekarar nan ta bana, tana atisaye da shiga gasanni a tsibirin Panglao na lardin Bohol dake tsakiyar kasar Philippines, Xu ta yanke shawarar ci gaba da zama a tsibirin, inda take ci gaba da horo, da horas da ‘yan wasa, wanda hakan ya zamewa wannan babbar ‘yar wasan nutso muhimmiyar dama ta samun kudin shiga.
Tsibirin Panglao, na da nisan kusan sa’a guda daga sanannen wurin yawon bude idon nan na “Chocolate Hills”, a yanzu haka ya zama muhimmin wuri na wasan nutso cikin ruwa, saboda kyakkyawan yanayin tekun sa, da kuma yanayi mai dumi na wurin.
Tsibirin yana da wurare masu kyan gani ga masu nutso ba tare da kayan taimakawa numfashi ba, da ma masu nutso ta amfani da bututun shakar numfashi. Yanzu haka sama da masu linkaya 100 daga sassan duniya daban daban na rayuwa a tsibirin Panglao, domin atisaye na yau da kullum, cik har da manyan kwararrun ‘yan wasan nutso irin su Alenka Artnik dan asalin kasar Slovenia.
Mazauna wurin wadanda mafi yawan su masu kamun kifi ne, suna karrama baki dake zuwa wannan wuri, saboda kamanceceniya da suke da ita a fannin sana’ar su ta kamun kifi da ‘yan wasan nutso.
Wani wanda ya ci gajiyar zama a tsibirin mai suna Lu Qing, wanda a da injiniyan fasahohin sadarwa ne daga kasar Sin, a yanzu yana jagorantar cibiyar horas da masu wasan nutso a tsibirin. Kaza lika Lu ya sha hada gasannin kasa da kasa daban daban, ciki har da na cin kofin Asiya, wanda masu wasan nutso ba kayan taimakawa numfashi da dama ke fatan lashewa.
Lu ya yi fatan zama kwararren mai wasan nutso, inda a shekarar 2017 ya bar garin sa wato Shenzhen na Sin ya koma tsibirin Panglao, a can ne ya mayar da hankali sosai ga wannan wasa. To sai dai kuma bai cimma nasarar da ya yi fata ba, don haka sai ya mayar da hankali ga shirya gasanni masu nasaba da wasa, kuma a wasu lokutan ya kan yi aikin kawar da hadurra ga masu gudanar da gasar nutso.
Kamar yadda Lu ya yi bayani, yanayin ban sha’awa na wannan wasa ya sauya rayuwarsa. Ya ce "Wasan nutso ba tare da kayan taimakawa numfashi ba, kusan wata hanya ce ta rayuwa mai cike da burgewa, wadda ke sanya masu shawarar wasan, da masu shiga a dama da su barin rayuwar su ta ainihi, su dawo wannan tsubiri suna rayuwa mai sauki, da da’ar zamantakewa. A gani na baiwa zuciya cikakkiyar nutsuwa shi ne matakin farko na koyon nutso ba tare da kayan taimakawa numfashi ba. Dole ne mutum ya samu cikakkiyar nutsuwar jiki yayin da yake son sarrafa shi. Don haka, shekaru da matakin nutsuwa, kusan su ne fifikon da masu wasan nutso ba tare da kayan taimakawa numfashi ba ke bukata".
A watan Mayun da ya gabata, ‘yar wasan nutso daga kasar Italiya mai shekaru 31 da haihuwa Alessia Zecchini, ta kafa sabon tarihin zama zakara a ajin wasan nutso na CWT, a gasar da aka gudanar a Panglao, inda ta karya matsayin bajimta na nutson mita 123.
Xu, wadda ta girmi Zecchini da shekaru 4, ta ce wannan matsayin bajimta da Zicchini ta kafa, buri ne na dukkanin ‘yan wasan nutso, ko da yake wasan nutso ba tare da kayan taimakawa numfashi ba, takara ne da mutum ke yi da kan sa, ba wai da wani mutum na daban ba.
Xu ta ce "Na ji dadin yadda na kara kyautata dabarata ta yin numfashi a waje kafin yin nutso. A halin yanzu, ina jin kamar ni kadai ce a duniya".
Bisa adadin atisayen da take yi a kullum, Xu tana fatan kaiwa ga yin nutson mita 120 a shekarar badi. To sai dai kuma, ba ta fitar da ran kalubalantar gwarzuwa Zecchini ba.
A cewar Xu, "Ba batun gasa ne da wani mutum kadai ba; fata na kawai shi ne matsayin bajimta ta ya shiga kundin kwararru na duniya".