Kasar Sin mai burin ganin ci gaban kowa
2023-09-26 17:09:17 CMG Hausa
Da safiyar yau Talata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar da takardar bayani mai taken “Al’ummar duniya mai makoma ta bai daya: Shawara da matakan kasar Sin,” wadda ta yi cikakken bayani game da yadda za a karfafa dunkulewar dukkanin bil adama.
Takardar ta tabo wasu muhimman batutuwa da suka ja hankalina, nake ganin ya kamata al’ummar kasa da kasa su fahimta dangane da shawarar gina kyakkyawar makomar bil adama ta bai daya.
Na farko: Gabatar da sabuwar dabarar huldar diflomasiyya. Tabbas huldar kasa da kasa na cikin wani yanayi mai wuyar fahimta. Maimakon hada kai da zama masu ceton juna, sai ake fuskantar rarrabuwar kawuna da neman samun nasara daga faduwar wata kasa. Abubuwa da dama sun riga sun nuna mana cewa, babu wata kasa da za ta iya shawo kan kalubalen duniya ita kadai. A wannan gaba, takardar ta Sin ta nemi kasa da kasa su yi la’akari da cewa makomarsu na hade da juna, don haka kamata ya yi su hade kansu domin samun moriyar juna. Hakika, wannan ita ce hanya daya tilo mai bullewa, domin dabaru na mulkin danniya da babakere, ba su amfani duniyarmu da komai ba sai fitina da rashin zaman lafiya da talauci da sauransu.
Na biyu: Samar da sabbin dabarun shugabantar duniya.
A cewar takardar, makoma ta bai daya ta bil adama, ita ce samun duniya mai daidaito da adalci da gaskiya. Hakika dukkanin bil adama ba su da bambanci. Misali, a lokacin annobar COVID-19, annobar ba ta kama mutane bisa launi ko addini ko kabilarsu ba. Wannan na kara tabbatar da cewa, babu wanda da ya fi wani. Haka kuma babu wata kasa da ta fi wata. Don haka bai kamata wata ko wasu ’yan tsiraru su wa duniya babakere ko su rika cin zalin wasu ba. Manufar kasar Sin ita ce, a tabbatar da daidaito da adalci da tsare gaskiya domin a gudu tare a tsira tare, a kuma kai ga samun duniya mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.
Na uku: samar da sabbin damarmakin musaya tsakanin kasa da kasa.
Kamar yadda Mal. Bahaushe kan ce, “Hannu daya ba ya daukar jinka”, shawarar kasar Sin a nan ita ce, inganta cudanyar kasa da kasa bisa daidaito da adalci da musaya tsakanin al’ummominsu. Babban abun dake kawo sabani, a ganina shi ne, rashin fahimta. Inganta musaya tsakanin al’ummomin kasa da kasa tabbas zai kara fahimtar da juna game da al’adu da dabi’u da yanayin juna. Haka kuma, musaya da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa zai bude wata sabuwar kafa ta samun ci gaba da koyi da juna, lamarin da zai sa kasashe su kasance masu mayar da hankali kan ci gaban juna maimakon neman ganin faduwarsu.
Na hudu: Gudunmawa da matakan kasar Sin.
A nan takardar ta kuma zayyano wasu daga cikin gudunmawar kasar Sin wajen cimma wannan buri, kamar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, shawarar ci gaban duniya, shawarar tsaron duniya, shawarar warware matsalar Ukraine da Rasha da sauransu. Wadannan duka shawarwari ne da kasar Sin ta gabatar da zummar kai wa ga samar da kyakkyawar makomar bil adama.
Wadannan batutuwa kadan ne daga cikin abubuwan da wannan takarda ta kunsa. Tabbas kasar Sin ba ta tsaya kan rayawa da neman inganta kanta. Har kullum, ba ta nuna son kai ko girman kai, burinta shi ne, ganin dukkan kasashen duniya sun samu ci gaba da zaman lafiya ta yadda bil adama za su yi zaman jituwa cikin wadata da kwanciyar hankali. Wannan ita ake kira da babbar kasar mai sowa kowa abun da take sowa kanta. (Faeza Mustapha)