logo

HAUSA

Al’adun kasar Sin na da tushen neman zaman lafiya tun lokacin da

2023-09-26 20:36:41 CMG

DAGA MINA

Wani muhimmin littafin gargajiya dake bayyana ra’ayoyin Confucius na kasar Sin ya nuna cewa, amfanin ladabi shi ne kyautata huldar mutane, wato tabbatar da jituwa da zaman lafiya tsakanin mutane daban-daban. Jituwa shi ne ka’ida mai tushe da Sinawa ke bi wajen daidaita huldar dake tsakanin daidaikun mutane da ma tsakanin Bil Adama da muhalli. Sinawa rungumar ra’ayin zauna lafiya da juna tsakanin ‘yan gida, sa’an nan sun kuma yayata ra’ayin zuwa cikin kasa har ma da duk fadin duniya baki daya.

Sinawa na gadar irin wannan ruhi daga kaka da kakanni, hakan ya sa ko a lokacin da Sin ta fi karfi a tarihi, ba ta taba kafa mulkin mallaka ko kai hare-hare ga sauran kasashe ba. Yin hakuri da mabambanta ra’ayi da ajiye sabani don tabbatar da jituwa, shi ne matsayin da Sin take dauka kan huldarta da kasashen waje.

Al’adar Sinawa ta kasance mai matukar son zaman lafiya da jituwa, shi ya sa kasar Sin ke kokarin taka rawarta wajen samar da zaman lafiya da jituwa da ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya gaba, da ma kiyaye tsarin duniya, hakan ya sa mutanen kasar Sin ke son yin mu’ammalar al’adu a maimakon yin babakere, kuma ba ta son dora ra’ayinta ko tsarin siyasa nata ga saura, kuma take tsayawa tsayin daka kan hada kanta da sauran sassan duniya a maimakon yin fito-na-fito da juna ko kafa kungiyoyin kawancen don mai da wasu saniyar ware. (Mai zana da rubuta: MINA)