Sin ta yi kira da a janyewa Venezuela takunkumai bisa kokarin kasar na kare hakkokin bil adama
2023-09-26 10:08:45 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa Chen Xu, ya jinjinawa kwazon gwamnatin Venezuela, a fannin kare hakkokin bil adama, yana mai cewa, kamata ya yi a dagewa kasar takunkumai na muzgunawa da aka kakaba mata.
Chen Xu, wanda ya yi kiran a jiya Litinin a birnin Geneva na kasar Switzerland, yayin taro na 54 na hukumar kare hakkokin bil adama ta MDD, yana mai cewa, kasar Sin ta gamsu da matakan gwamnatin Venezuela na yayatawa, da kare hakkokin bil adama. Kuma za ta ci gaba da goyon bayan gwamnati da al’ummar Venezuela, wajen kare ikon mulkin kai da martabar kasa.
Kaza lika, Sin za ta aiwatar da dukkanin matakan da suka kamata, na tallafawa wajen inganta rayuwar al’ummar Venezuela, da taimakawa kasar a bangaren kyautata matakan kare hakkokin al’ummar ta, bisa yanayin da kasar ke ciki, ta yadda za a kai ga kara yayatawa, da kare hakkokin jama’a. (Saminu Alhassan)